• English
  • Business News
Wednesday, May 14, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Okowa Ya Karbi Wadanda Suka Nemi Takarar Gwamnan APC Uku Da Suka Koma PDP A Sakkwato 

by Sharfaddeen Sidi Umar, Sokoto
3 years ago
in Siyasa
0
Okowa Ya Karbi Wadanda Suka Nemi Takarar Gwamnan APC Uku Da Suka Koma PDP A Sakkwato 
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Mataimakin Dan Takarar Shugaban Kasa a Jam’iyyar Adawa, PDP a zaben 2023, Ifeanyi Okowa, ya jagoranci karbar manyan jiga-jigan jam’iyyar APC da suka sauya sheka zuwa PDP a Sakkwato tare da bayyana cewar lokaci ya yi da za su ceto Nijeriya daga halin da APC ta jefa ta. 

Mataimakin na Atiku Abubakar a 2023, ya jaddada cewar canza shekar fitattun ‘yan siyasar daga jam’iyyar da ke mulkin kasa zuwa jam’iyyar adawa a karkashin jagorancin, gwamna jihar Aminu Waziri Tambuwal, babbar alama ce ta samun nasarar PDP kamar yadda ya bayyana a yammacin ranar Lahadi a Sakkwato.

  • Shugaba Xi Ya Jaddada Muhimmancin Jin Ra’ayoyin Jama’a Ta Hanyoyi Daban-Daban
  • Zargin Cire Sashen Jikin Yaro: Jami’ar Lincoln Ta Dakatar Da Ekweremadu

Ya ce a shekara mai zuwa mulkin Nijeriya zai koma a hannun jam’iyyar PDP wadda za ta kawar da matsalolin al’umma da inganta jin dadinsu.

Kana ya ce PDP za ta dawo da kima da martabar Nijeriya a idanun duniya.

Ya ce a yanzu lokaci ne na ceto Nijeriya kuma lokacin sake gina kasa, don haka ya zama wajibi a yi aiki tare domin kubutar da Nijeriya daga hannun wadanda ke kokarin ruguza ta.

Labarai Masu Nasaba

Rikicin Ribas: Fubara Ya Ce Ya San Yadda Zai Magance Matsalar, Ya Gargaɗi Magoya Bayansa

Wike Ya Gargaɗi PDP Kan Bai Wa Ɗan Arewa Takara A 2027

“Mun yadda da Nijeriya a matsayin kasa daya al’umma daya akasin wasu ‘yan takarar da ko kadan ba su yadda da ci gaba da dorewar kasar nan a matsayin kasa daya ba.

“Ya bayyana tare da cewar a bisa ga kwarewa da gogewa da sanin makamar shugabancin da Atiku Abubakar yake da ita zai jagoranci mulkin da kowa zai yaba a Nijeriya.”

Kusoshin ‘yan siyasar wadanda fitar su ta girgiza APC tare da karya lagonta a Jihar sun hada da uku daga cikin wadanda suka tsayawa jam’iyyar takarar fidda gwani na zaben gwamna, wato tsohon Ministan Wasanni kana Daraktan yakin neman zaben Buhari a 2019 a Sakkkwato, Yusuf Sulaiman, Shugaban Kwamitin Yaki da Fatara a Majalisar Wakilai, Hon. Abdullahi Salame da A.A Gumbi.

Haka ma akwai Kakakin Majalisar Dokoki ta Jihar Sakkwato, Hon. Aminu Achida da tsohon Ministan Al’adu, Sanata Bello Jibril Gada da kuma Hon. Yusuf Kurdula wanda ke wakiltar Tangaza/Gudu a Majalisar Wakilai.

Sauran sun hada da Hon. Murtala Maigona, wanda ke wakiltar Karamar Hukumar Wamakko a Majalisar Dokoki ta Jiha da tsofaffin shugabannin kananan hukumomin Sakkwato ta Arewa da Binji, Abdullahi Hassan da Sayyadi Nuhu Binji da tsofaffin kwamishinoni Aminu Bello Sokoto da Dahiru Maishanu Yabo.

Sai Mataimaki na Musamman ga Sanata Aliyu Wamakko kan Yada Labarai, Hassan Sahabi Sanyinnawal, da Yahaya Dallatu da ‘yan siyasa, ‘yan kasuwa, ‘yan kwangila da dubban daruruwan magoya bayansu.

A jawabinsa, tsohon Ministan Wasanni, Yusuf Sulaiman, ya bayyana cewar canza shekarsu daga APC zuwa PDP abin murna ne kuma za su jajirce domin ganin PDP ta samu nasarar kafa gwamnati daga sama har kasa baki daya.

Ya ce 2023 lokaci ne da jam’iyyar PDP za ta sake komawa fadar mulkin kasa.

Gwamna Aminu Waziri Tambuwal a takaitaccen jawabinsa, ya bayyana cewar a bisa ga kasawar APC na magance matsalolin da suka dabaibaye Nijeriya, wajibi ne a 2023 al’umma su zabi PDP domin kai kasar nan a tudun mun tsira.

Ya ce APC ba ta da tsari da cancantar da za ta kawar da matsalolin ‘yan Nijeriya.

Ya ce sakon da fitar manyan ‘yan siyasar ke nunawa a bayyane yake na kyakkyawar makoma da ke a gaban PDP wadda ya ce ba za ta yi kasa a guiwa ba wajen shimfida ingantaccen mulki na gari wanda ‘yan Nijeriya za su yaba a karkashin jagorancin Wazirin Adamawa.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: APCAtiku AbubakarOkowaPDPSakkwatoSauya ShekaTambuwalZaben 2023
ShareTweetSendShare
Previous Post

Shugaba Xi Ya Jaddada Muhimmancin Jin Ra’ayoyin Jama’a Ta Hanyoyi Daban-Daban

Next Post

Har Yanzu Ina Neman Abokin Takara — Tinubu

Related

Rikicin Ribas: Fubara Ya Ce Ya San Yadda Zai Magance Matsalar, Ya Gargaɗi Magoya Bayansa
Labarai

Rikicin Ribas: Fubara Ya Ce Ya San Yadda Zai Magance Matsalar, Ya Gargaɗi Magoya Bayansa

1 day ago
Wike Ya Gargaɗi PDP Kan Bai Wa Ɗan Arewa Takara A 2027
Siyasa

Wike Ya Gargaɗi PDP Kan Bai Wa Ɗan Arewa Takara A 2027

1 day ago
NNPP Ta Yi Asarar Ɗan Majalisa A Kano, Ya Koma APC
Siyasa

NNPP Ta Yi Asarar Ɗan Majalisa A Kano, Ya Koma APC

2 days ago
Uwargidan Jonathan Ta Bayyana Goyon Bayanta Ga Remi Tinubu
Siyasa

Uwargidan Jonathan Ta Bayyana Goyon Bayanta Ga Remi Tinubu

3 days ago
Martanin Kwankwaso Ga Kawu Sumaila Da Sauran Masu Ficewa Daga NNPP
Siyasa

Martanin Kwankwaso Ga Kawu Sumaila Da Sauran Masu Ficewa Daga NNPP

4 days ago
Dalilin Gwamnatin Kano Na Haramta Shirye-shiryen Siyasa Kai Tsaye
Siyasa

Dalilin Gwamnatin Kano Na Haramta Shirye-shiryen Siyasa Kai Tsaye

6 days ago
Next Post
Har Yanzu Ina Neman Abokin Takara — Tinubu

Har Yanzu Ina Neman Abokin Takara — Tinubu

LABARAI MASU NASABA

Ɗan Wasan Super Eagles Na Tsaka Mai Wuya Bayan An Yi Masa Tiyata

Ɗan Wasan Super Eagles Na Tsaka Mai Wuya Bayan An Yi Masa Tiyata

May 14, 2025
Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Bunƙasa, Amma Farashin Kayayyaki Na Ci Gaba Da Tashi – Bankin Duniya

Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Bunƙasa, Amma Farashin Kayayyaki Na Ci Gaba Da Tashi – Bankin Duniya

May 14, 2025
Sin Ta Daidaita Harajin Fito Kan Hajojin Amurka Da Ake Shigarwa Kasar

Sin Ta Daidaita Harajin Fito Kan Hajojin Amurka Da Ake Shigarwa Kasar

May 14, 2025
Amurka Da Saudiyya Sun Ƙulla Yarjejeniyar Dala Biliyan 600 Kan Tsaro, Makamashi Da Fasaha

Amurka Da Saudiyya Sun Ƙulla Yarjejeniyar Dala Biliyan 600 Kan Tsaro, Makamashi Da Fasaha

May 14, 2025
Peng Liyuan Da Uwar Gidan Shugaban Kasar Brazil Sun Ziyarci Babban Zauren Nuna Fasahohin Nishadantarwa Ta Kasar Sin

Peng Liyuan Da Uwar Gidan Shugaban Kasar Brazil Sun Ziyarci Babban Zauren Nuna Fasahohin Nishadantarwa Ta Kasar Sin

May 14, 2025
‘Yansanda Sun Kama Masu Laifi 239, Sun Ƙwato Makamai Da Alburusai A Kogi

‘Yansanda Sun Kama Masu Laifi 239, Sun Ƙwato Makamai Da Alburusai A Kogi

May 14, 2025
Dakarun Soji Sun Daƙile Wani Sabon Harin ISWAP A Dikwa

Dakarun Soji Sun Daƙile Wani Sabon Harin ISWAP A Dikwa

May 14, 2025
Sojoji 20 Sun Ɓace Bayan Harin Da ISWAP Suka Kai Marte

Sojoji 20 Sun Ɓace Bayan Harin Da ISWAP Suka Kai Marte

May 14, 2025
Ko Kanawa Za Su Yafe Wa Ganduje?

Kotu Ta Ce Za A Ci Gaba Da Shari’ar Ganduje Kan Zargin Aikata Rashawa A Kano

May 14, 2025
Binciken Jin Ra’ayoyi Na CGTN: Ma’aikatar Harkokin Wajen Sin Ta Ce Harajin Fentanyl Ya Gurgunta Hadin Gwiwar Amurka Da Sin Kuma Fiye Da Kashi 90% Na Jama’a Sun Koka Da “Jarabar” Amurka Ta Cin Zarafi

Binciken Jin Ra’ayoyi Na CGTN: Ma’aikatar Harkokin Wajen Sin Ta Ce Harajin Fentanyl Ya Gurgunta Hadin Gwiwar Amurka Da Sin Kuma Fiye Da Kashi 90% Na Jama’a Sun Koka Da “Jarabar” Amurka Ta Cin Zarafi

May 13, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.