Kungiyar kasashe masu arzikin mai (OPEC) ta tsawaita rage adadin mai da ake hakowa, domin ganin ta inganta kasuwancin mai din, amma ta sanya ranar fara kawo man kasuwar yanar gizo a wannan shekarar.
Haka kuma OPEC ta tsaiwata wa Nijeriya ci gaba da hako ganga mililiyan 1.5 a kowace rana har zuwa 2025. OPEC ta sanar da hakan a taronta karo na 37.
- Baya Ta Haihu: INEC Ta Rushe Babban Taron Jam’iyyar LP Na Kasa
- Wasu Hakkokin Miji Da Suka Kamata Mata Su Mayar Da Hankali A Kai
An cimma yarjejeniyar ne a Riyadh a ranar Lahadi, lamarin da ya zarce yadda ake tsammani. Sannan, kungiyar za ta fara juya man da aka samu a watan Oktoba.
Yarjejeniyar na da manufar taimaka wa farashin mai kan yadda farashi ya mabanbanta, yayin da wasu ke da farashi mai sauki wasu kuma nasu da tsada.
“Za mu ci gaba da taka-tsantsan da tsare-tsaren,” cewar ministan makamashin Saundiyya, Prince Abdulaziz bin Salman kamar yadda ya shaida wa ‘yan jarida bayan taron. Hakan ya hada da matakin dakatarwa ko rage yawan man da ake fitarwa.
Farashin danyen mai ya ragu a ‘yan kwanain baya duk da halin da tattakin arzikin ke ciki a kasa mafi girma wajen amfani da man wato Chine da kuma sanya kokonto kan kudin ruwa na wasu kasashe. An samu ganga guda kan dala 81.62 a zuwa ranar 31 ga watan Mayu, lamarin da ya garu da kaso 7.1 a wata guda.