A kasa da awa 24 kafin fara gudanar da zaben kujerar gwamna a jihar Osun, an hangi wasu da ake zargin bata-gari ne na yawo da bindigu a garin Osogbo.
In za a iya tunawa, tuni Sufeto-Janar na ‘yan sanda, Usman Alkali Baba, ya bayar da umarni a tura mataimakansa hudu zuwa da Kwamishinonin ‘yan sanda hudu da mataimakan Kwamishinonin ‘yan sanda 15 da kuma wasu mataimakan ‘yan sanda 30 zuwa jihar don su tabbatar da tsaro a lokacin gudanar da zaben.
- Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rajistar Hakar Ma’adanai Ba Sai Da Katin Zabe -Babangida
- Mai Gadin Kabarin Manzon Allah SAW Ya Rasu
Alkali ya kuma gudanar da taro da masu ruwa da tsaki a Osogboa, inda ya sanar da cewa jami’an ‘yan sanda 21,000 aka tura zuwa jihar don su tabbatar da tsaro a lokacin zaben.
Sai dai, a jiya Alhamis a wani gangamin yakin neman zaben da jam’iyyar PDP ta yi a garin Osogbo, an ga wasu ‘yan bangar siyasa na wasa da miyagun makamai a gaban jami’an tsaro.
Hakan ya biyo bayan dan takarar gwamna Sanata Ademola Adeleke ya kammala jawabinsa a gurin taron.
Haka zalika, a wurare daban-daban a Osogbo an ga wasu mutane dauke da bindigu suna hutawa a wani rukunin gidaje kusa da wata mashayar giya.