A yayin da al’ummar jihar Osun suka fito a yau Asabar don zabar sabon gwamnan jihar da zai yi wa’adin shekara hudu a karagar mulkin jihar, an tura jami’an tsaro da dama don su wanzar da tsaro.Â
Kimanin masu jefa kuri’a guda 1,955,657 ne suka yi rijista a jihar wadanda kuma ake sa ran za su kada kuri’unsu a rumfunan zabe guda 3,763.
- Zaben Osun: ‘Yan Nijeriya Na Kallon Mu – Mahmoud Ga Ma’aikatan INEC
- 2023: INEC Za Ta Rufe Rajistar Katin Zabe A Karshen Watan Yuli
Sai dai wasu daga cikin masu kada kuri’ar sun lashi takobin cewa za su karbi kudaden ‘yan takarar sannan su zabi ‘yan takarar da suke so.
Daya daga cikin masu kada kuri’ar ya ce, zabar ‘yan takarar ya danganta ne da irin yawan kudaden da suka bai wa masu kada kuri’un.
Shi ma wani mai kada kuri’a Kunle Ogundele, ya sanar da cewa duk da dimbin jami’an tsaro da aka garke a guraren jefa kuri’un masu kada kuri’a za su fito da yawansu.
Kunle Ogundele ya kara da cewa masu kada kuri’un a shirye suke su jefa kuri’unsu musamman domin su zabi ‘yan takarar da suke da bukata.