A yau talata ne, kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jamiyyar LP ya sanar da cewa, ya nada Akin Osuntokun, a matsayin sabon dakaraktan kwamitin yakin neman Obi da Datti na neman shugabancin kasar nan a zaben 2023.
An nada Osuntokun ne biyo bayan ajiye mukamin da Dakta Doyin Okupe ya yi bayan an yanke masa hukuncin safarar kudade.
Shugaban jamiyyar na kasa Barista Julius Abure ne ya sanar da nadin a Abuja a taron da jamiyyar ta gudanar a tsakanin masu ruwa da tsaki da ‘yan takarar kuma
Ya ce, kafin nadin na Osuntokun ya kasance shine jami’in shiyya na PCC na jamiytar LP a kudu maso gabas kuma zai iya yin amfani da kwarewarsa don ganin Obi da Datti sun samu nasara a zaben na shugaban kasa.
Okupe dai ya aje mukamin na sa ne saboda hukuncin da babbar kotun Abuja ta yanke masa akan karbar naira miliyan 200 na kudin makamai daga gun tsohon mai bayar da shawara a fannin tsaro Sambo Dasuki.
Osuntokun dan jarida ne, marubuci kuma kwararre a fannin siyasa.
Ya kuma kasance tsohon shugaban sashen labarai na kamfanin dillancin labarai na kasa ya kuma taba rike mukamin a baya, tsohon mai baiwa tsohon shugaban kasa Cit Olusegun Obasanjo shawara a harkar siyasa.
Ya kuma taba rike mukamin daraktan kwamitin yaken neman zaben PDP a 2011.