Gwamnan Jihar Osun, Ademola Adeleke, ya ce, tsohon gwamnan Jihar da ya bar masa kujera, Gboyega Oyetola, ya yi gaba gadi kawai ya je ya lafto bashin naira biliyan 18 jim kadan bayan da ya fadi a zaben gwaman jihar da aka gudanar a ranar 16 ga watan July na 2022.
Gwamnan ya ce, kudaden da Oyetola ya ciwo bashinsu bayan fadinsa zabe ba su san ina ya kai ko me ya yi da su ba.
Bisa hakan, gwamnan ya ce gwamnatinsa ta gaji bashin biliyan 407.32 zuwa watan Nuwamban 2022.
Adeleke ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis sa’ilin da ke ganawa da sarakunan gargajiya na jihar Osun a Osogbo babban birnin jihar Osun ranar Alhamis.
A cewarsa, “Gwamnatina ta gaji basukan da ake bin jihar kashi-kashi har guda takwas da suka kunshi bashin albashi, tulin basukan fansho da sauransu da Gwamnatin Oyetota ta bar mana.”
“Zuwa yau ana bin jihar Osun bashin biliyan N331.32.
“Idan aka hada da basukan albashi da fansho na naira biliyan 76. Basukan za su kai biliyan N407.32. Kuma har yanzu ba a tantance nawa ‘yan kwangila ke bi ba.
“Iyaka abun da ya shigo lalitar Gwamnatin jihar zuwa ranar Litinin 29 ga watan Nuwamba, kawai albashin watan Nuwamban 2022. Bayan hakan, lalitar jihar ya kasance wayam ba komai a ciki.
“A matsayina na gwamna, zan yi tambaya a madadinku. Kuma gaskiya muna bukatar amsa,” Adeleke ya fada wa sarakuna.
Ya kara da cewa, “Gwamnatin Oyetola dole ya fito ta yi bayanin bashin biliyan 331 da ta ciwo a madadin al’ummar jihar Osun me suka yi da shi da yaya suka kashe, ba tare da wani kwakkwaran aikin bunkasa jihar ba amma an ciwo tulin basuka.
“Kuma tilas ne gwamna Oyetola ya fito ya yi bayanin me ya yi da biliyan 18 da ya ciwo bashinsu bayan fadinsa a zabe ranar 16 ga watan July na 2022. Ya aka yi da su kuma ta yaya aka kashe su.
“Sannan, dole ya fito ya yi bayanin yadda aka yi jihar ya zama ana binta bashin albashin har naira biliyan 76 duk da cewa jihar ta samu kudaden Bail out na naira biliyan 50 daga wajen gwamnatin tarayya.”