Jigo a jam’iyyar PDP, Samuel Anyanwu, ya ce duk da rikicin da jam’iyyar ke fama da shi, PDP ba ta mutu ba kuma za ta farfaɗo.
Ya bayyana haka ne a shirin siyasa na gidan talabijin na Channels a ranar Litinin.
- Gwamnatin Sin Ba Ta Taba Bukatar Kamfanoni Su Tattara Ko Adana Bayanai Ba Bisa Ka’ida Ba Kuma Ba Za Ta Yi Hakan Ba
- Sin Ta Bayyana Damuwa Dangane Da Matakin Amurka Na Ingiza Daftarin Tsawaita Aikin Tawagar UNISFA
Anyanwu, wanda ya taɓa tsayawa takarar gwamnan Imo, ya ce yana da tabbacin PDP za ta magance matsalolinta.
“PDP ba ta mutu ba, kuma PDP ba za ta mutu ba,” in ji shi.
Ya kuma kare dangantakarsa da Ministan Abuja, Nyesom Wike, duk da sukar sa da ake yi.
“Lokacin da Wike, Makinde, Ugwuanyi, Ikpeazu da Ortom suka kafa G5, bana are da su. Amma duk da haka, Wike abokina ne sosai. Lokacin da PDP ta samu matsala Wike ne ya yi ƙoƙarin tallafa mata,” in ji Anyanwu.
Ya ƙara da cewa Wike bai fice daga PDP ba.
Anyanwu ya kira taron gangamin PDP da aka yi a Ibadan a matsayin ɓata lokaci, yana mai cewa ba a yi sa bisa ƙa’ida ba.
Ya ce dakatar da shi daga matsayin Sakataren jam’iyyar na Ƙasa ba a kan ka’ida yake ba saboda jam’iyyar ba ta bi umarnin kotu ba.
Ya kuma ce taron bai haɗa jihohi da dama ba, don haka bai samu cikakken goyon baya ba.
A yayin babban taron na PDP na 2025, jam’iyyar ta kori Wike, tsohon gwamnan Ekiti Ayodele Fayose, Samuel Anyanwu da wasu, bisa zargin cin amanar jam’iyyar.
Haka kuma ta rushe shugabancin jam’iyyar a Imo, Abia, Enugu, Akwa Ibom da Ribas.
Bode George, wani jigo a jam’iyyar PDP ne, ya gabatar da ƙudirin korar manyan mambobin 11, kan zarginsu da gudanar da abubuwan suka saɓa wa dok6 jam’iyya.
Shugaban PDP na Jihar Bauchi ya mara masa baya.














