Gwamnan Jihar Oyo, Injiniya Seyi Makinde, ya bayyana cewa ficewar tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar daga jam’iyyar PDP ba zata haifar da wani giɓi ba a jam’iyyar.
Makinde, yayin zantawa da manema labarai a taron cika shekaru 10 na Deji na Akure, Oba Aladetoyinbo Aladelusi, ya bayyana ficewar Atiku da cewa “zasu gode da ficewar guba,” yana mai cewa idan wani yana hana PDP ci gaba, ya fi dacewa ya fice.
- Ina Da Ƙwarewar Da Zan Iya Zama Shugaban Ƙasar Nijeriya – Makinde
- Farashin Kayayyaki Sun Sauka A Watan Yuni 2025
Ya ce, “Siyasa wasa ne na maslaha. Ficewar Atiku ba zata yi wa jam’iyyar PDP wata illa ba. PDP gida ne da kowa zai iya shiga kuma ya fita. Duk wanda ke hana ci gaba, ficewarsa tafi alheri.”
Gwamnan ya kuma bayyana cewa bai ɗauki jam’iyyar ADC a matsayin barazana ga PDP ba. A cewarsa, “masu mulki za su zo su tafi, amma ƙasa da al’umma za su ci gaba da wanzuwa.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp