Jam’iyyar PDP mai adawa a reshen Jihar Kebbi, ta dakatar da dakatar da dan takararta Malam Haruna Sa’idu-Dandi’o, na mazabar Kebbi ta Tsakiya bisa zargin yi wa jam’iyyar zagon kasa.
Shugabanin mazabar ta 1 ta Nasarawa da ke a Karamar Hukumar Birnin-Kebbi ne suka dakatar da Sai’du-Dandi’o.
- Farashin Gas Din Girki Ya Kara Yin Tashin Gwauron Zabi — NBS
- Mai Damfara Da Sunan Mace A Facebook Ya Shiga Hannun ‘Yan Sanda A Kano
Dakatarwar na kunshe ne a cikin sanarwar da shugaban mazabar Ibrahim Abdullahi-Na-Mazaba da sakatarensa Nasiru Aliyu, suka bai wa manema labarai a Birnin-Kebbi a ranar Lahadi.
In za a iya tunawa tun da farko, Sa’idu-Dandi’o, ne ya lashe zaben fidda gwani na mazabar ta tsakiya ba tare da hamayya ba.
Amma ana jiran hukuncin da zai biyo baya, bayan da ake zarginsa da yi wa jam’iyyar zagon kasa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp