Sakamakon taron koli na kwamitin zartarwa, PDP ta sha alwashin warware duk wani rikicin shugabanci da ya dabaibaye jam’iyyar a watan Agusta, inda ta bayar da umurnin cewa Umar Damagum ya ci gaba a matsayin mukaddashin shugaba.
Rahotanni sun bayyana cewa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Atiku Abubakar da ministan Abuja, Nyesom Wike sun kasance a wurin taron amma ba su ce uffan ba bayan kammala taron.
- Dalilin Da Ya Sa Duniya Ke Bukatar Karfin Sin Na Samar Da Hajoji Masu Alaka Da Makamashi Mai Tsafta
- Masu Zargin Uba Sani Kan Bashin el-Rufa’i Sun Jahilci Aikin Majalisa – Barista Bello
Da yake ganawa da manema labarai bayan kammala taron, Gwamnan Jihar Bauchi kuma shugaban kungiyar gwamnonin PDP, Bala Muhammad ya bayyana cewa jam’iyyar za ta warware duk wani rikicin shugabanci.
Ya ce, “Nan da watanni biyu, za ku ga ayyukan jam’iyyar sun sauya. Shugabanci nauyi ne mai matukar wahala. A duk lokacin da muka samu nasarar gudanar da babban taro, za mu duba batun rikicin shugabanci, sannan za mu duba kundin tsarin mulkin jam’iyyar.
Sai dai kuma yankin arewa ta tsakiya ya dage wajen ganin ya kammala wa’adin mulkin Iyorchia Ayu wanda aka dakatar da shi. Yankin bai ji dadin yadda aka ce Damagum ya ci gaba da jagorancin jam’iyyar har a samu nasarar gudanar da babban taro.
Sakataren yada labarai na jam’yyar PDP, Debo Ologunagha ya ce saboda a samu damar shulhuntawa, za a warware rikicin shugabanci a watan Agusta lokacin da ake tsammanin kwamitin zartarwa zai sake zama.
“Jam’iyyarmu ta jaddada muhimmancin sulhu da samun daidaito a tsakanin ‘ya’yan jam’iyyar a wannan lokaci. Kafin warware rikicin shugabanci, Umar Damagum zai ci gaba da rikon mukamin mukaddashin shugaba har zuwa ranar 15 ga Agustan 2024 lokacin da kwamitin zartarwa zai sake zama,” in ji Ologunagba.