Jam’iyyar adawa ta PDP ta yi kira ga Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya ƙaddamar da bincike kan tiriliyan 25 da ta zargi cewa wasu shugabanni da jami’an gwamnatin APC sun sace.
PDP ta yi wannan kiran ne a cikin wata sanarwa ta sabuwar shekara da kakakinta na ƙasa, Debo Ologuagba, ya fitar ranar Talata.
- Zimbabwe Ta Soke Yi Wa Masu Manyan Laifuka Hukuncin Kisa
- Sojin Ruwa Sun Yi Alƙawarin Ƙara Haƙo Gangar Mai Miliyan 3 A Kowace Rana
Sanarwar ta ce: “Dole shugaban ƙasa ya nuna jajircewarsa wajen yaƙi da cin hanci da rashawa ta hanyar bayar da umarnin yin bincike da dawo da tiriliyan 25 da aka ce wasu shugabannin APC sun wawure.”
Haka kuma, PDP ta nemi Tinubu ya bayyana adadin kuɗaɗen da aka tara daga cire tallafin man fetur tun lokacin da gwamnatinsa ta ɗauki wannan matakin a watan Mayun 2023.
Bugu da ƙari, jam’iyyar ta buƙaci shugaban ya kawo ƙarshen matsalolin tsaro, yunwa, da ƙarancin man fetur domin rage wahalhalun da ‘yan Nijeriya ke fuskanta.