Jam’iyyar PDP ta yi Allah-wadai da harin da aka kai wa wata makaranta ‘yan mata a Jihar Kebbi.
A yayin kai harin, maharan sun kashe mataimakin shugaban makarantar, tare da sace ɗalibai 25.
- PDP Ba Ta Mutu Ba Duk Da Rikicin Da Ta Ke Fama Da Shi – Anyanwu
- ’Yansanda Sun Tura Tawaga Don Ceto Ɗaliban Da Aka Sace A Kebbi
PDP ta ce wannan lamari mai ban tausayi yana nuna yadda rashin tsaro ya ƙara ƙamari a Nijeriya.
Jam’iyyar ta zargi gwamnati, ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Tinubu, da rashin kare jama’a.
Jam’iyyar ta bayyana cewa idan gwamnati ta gaza kare jama’arta, to dole ne ta ɗauki alhakin kuma ta magance matsalar, ba ta yi watsi da ita ba.
PDP ta jajanta wa iyayen ɗaliban da aka sace da kuma iyalan mataimakin shugaban makarantar da aka kashe.
Ta kuma aike saƙon ta’aziyyarta ga makarantar da gwamnatin Jihar Kebbi.
Jam’iyyar ta nuna damuwa kan yadda sace-sacen mutane a jihohi kamar Nasarawa, Filato, Kano, da Katsina suka yawaita a baya-bayan nan.
Saboda haka, PDP ta yi kira ga shugaba Tinubu da ya san yadda zai kare rayuka da dukiyoyim al’ummar Njeriya domin a kawo ƙarshen matsalar.














