Jam’iyyar PDP ta Jihar Kogi ta ƙi amincewa da sakamakon zaɓen cike gurbi na Okura da aka gudanar a ranar 16 ga Agusta, 2025, tana mai cewa an yi maguɗi kuma “abin kunya ne ga dimokuraɗiyya.” Jam’iyyar ta nemi a soke zaɓen nan take tare da shirya sabon zaɓe bisa tsarin doka.
A cikin wata sanarwa da shugaban PDP na jihar, Enemona Anyebe, ya sa wa hannu, PDP ta zargi jam’iyyar APC mai mulki da haɗin gwuiwa da jami’an tsaro, da ƴan daba da kuma wasu jami’an INEC wajen murɗe zaɓen. Ta ce sama da kashi 98% na rumfunan zaɓe ba a gudanar da zaɓe a cikinsu ba, inda aka raba kayan zaɓe zuwa wurare daban-daban da ba a sani ba.
- Sojoji Sun Ceto Shugaban Fulani, Mutane 5 Daga Hannun Ƴan Bindiga A Kogi
- Ƴan Bindiga Sun Sace Fasinjoji 9 A Kogi
Jam’iyyar ta yi Allah-wadai da sakamakon da INEC ta bayyana na bai wa APC ƙuri’u 55,073, PDP kuma ƙuri’a 1,038, tana mai cewa wannan ba zai yiwu ba saboda a zaɓen 2023 APC ta samu 8,549 yayin da PDP ta samu 1,487. PDP ta ce sakamakon yanzu ya nuna “babban maguɗi da tafka da warwara” musamman ganin REC ya bayyana a AIT cewa akwai ƙarancin fitowar masu zaɓe ranar zaɓen.
PDP ta bayyana matakan da za ta ɗauka ciki har da ƙin amincewa da sakamakon, da buƙatar soke shi baki ɗaya da kuma shirya sabon zaɓe bisa ga tanadin kundin tsarin mulki da dokar zaɓe ta 2022. Jam’iyyar ta yi kira ga shugabannin ta da magoya baya da su kwantar da hankali, tare da jaddada cewa za ta bi matakan doka da lumana har sai an samu adalci.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp