Jam’iyyar PDP ta soki dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC Sanata Bola Tinubu da kuma shugabannin Jam’iyyar bisa karkatar da sabbin takardun kudi don saye kuri’u a zaben 25 ga watan Fabrairun 2023.
Jam’iyyar PDP ta bayyana fatanta da cewa, idan dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP Alh. Atiku Abubakar ya lashe zaben, zai tsamo kasar daga cikin halin da gwamnatin APC ta jefa ta.
Sakataren yada labarai na kasa na jam’iyyar PDP Debo Ologunagba wanda ya bayyana hakan a cikin sanarwar da ya fitar, ya nuna takaicinsa akan halin kuncin da karancin sabbin kudaden suka jefa ‘yan Nijeriya a ciki.
Ya yi ikirarin cewa, shugabanin jam’iyyar APC ne suka karkatar tare da boye sabbin kudaden don su yi amfani da su wajen sayan kuri’u a ranar 25 ga watan fabirairu 2023.
A cewarsa, ‘yan Nijeriya a yanzu sun farga sun kuma gano gaskiya cewa akwai hannun Asiwaju da shugabanin APC a cikin karancin sabbin takardun kudaden da suke ci gaba da fuskanta.
Ya gargadi bankin na CBN da ya bi a sannu akan mawuyacin halin da ya jefa ‘yan Nijeriya a ciki saboda karancin sabbin kudaden.