Uwar gidan shugaban kasar Sin Xi Jinping, Peng Liyuan ta gana da Sylvia Bongo Ondimba, uwar gidan shugaban kasar Gabon, wadda ta yi wa mai gidanta rakiya a ziyararsa a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin.
Yayin ganawar, Peng Liyuan ta yaba da kokarin da Sylvia ta dade tana yi kan aikin tallafawa jama’a, tare da yin bayani kan sakamakon da kasar Sin ta samu a fannonin magancewa da jinyar cutar Aids da cutar tarin fuka, da kandagarkin cutar COVID-19. Ta kuma bayyana cewa, kasar Sin tana son kara karfafa cudanya da more fasahohin tsakaninta da kasar Gabon, domin ingiza hadin gwiwar dake tsakaninsu, ta yadda za su amfanawa al’ummomin kasashen biyu.
A nata bangare, Sylvia Ondimba, ta bayyana cewa, kasarta ta Gabon tana jinjinawa babban sakamakon da kasar Sin ta samu a bangaren kiwon lafiyar jama’a, don haka tana son koyon fasahohin da kasar Sin ta samu tare kuma da kara karfafa hadin gwiwar dake tsakaninta da kasar Sin. (Mai fassarawa: Jamila)