Da yammacin jiya Laraba, uwargidan shugaban kasar Sin Peng Liyuan ta gana da uwargidan shugaban kasar Uzbekistan Ziroatkhon Mirziyoyeva a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin. A wannan rana kuma, shugaban kasar Uzbekistan Shavkat Mirziyoyev ya kai ziyarar aiki a kasar Sin.
A yayin ganawar tasu, madam Peng Liyuan ta nuna yabo matuka ga madam Ziroatkhon Mirziyoyeva dangane da kokarin da ta bayar kan harkokin jin kai da na tallafawa al’umma. Tana fatan habaka hadin gwiwa a tsakanin bangarorin biyu wajen kare ’yancin mata da yara da kuma masu bukata ta musamman, ta yadda za a tallafa wa al’ummomin kasashen biyu yadda ya kamata.
- Xi Jinping Ya Yi Jawabi Ta Kafar Bidiyo Ga Liyafar Murnar Cika Shekaru 60 Da Kulla Huldar Diplomasiyya A Tsakanin Sin Da Faransa
- CMG Ya Rattaba Hannu Kan Yarjejeniyar Hadin Gwiwa Da Hukumar Watsa Labaran Antigua Da Barbuda
Peng Liyuan ta ce, cikin ’yan shekarun nan, musayar al’adu na bunkasuwa da sauri a tsakanin kasashen biyu, ana fatan ci gaba da zurfafa zumuncin dake tsakanin jama’ar kasashen biyu bisa tushen zumuncin gargajiyar da aka kulla tsakanin bangarorin biyu.
A nata bangare kuma, Ziroatkhon Mirziyoyeva ta nuna yabo matuka dangane da muhimmiyar rawa da madam Peng ta taka a fannin raya harkokin dake da nasaba da mata da yara. Tana son ci gaba da zurfafa hadin gwiwar dake tsakanin bangarorin biyu kan ayyukan, yayin ba da gudummawa domin zurfafa huldar abokantaka a tsakanin kasashen biyu. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)