Da safiyar yau Alhamis ne mai dakin shugaban kasar Sin Peng Liyuan, ta halarci taron karawa juna sani game da raya ilimi na Sin da Afirka, tare da matan shugabannin kasashen Afirka, mai taken “Sin da Afirka na hada hannu wajen ilmantarwa da karfafa wadatar mata”.
Yayin taron wanda ya gudana a nan birnin Beijing, Peng Liyuan, wadda ita ce wakiliyar musamman ta hukumar raya ilimi, kimiyya da al’adu ta MDD UNESCO, mai lura da fannin raya ilimin ‘ya’ya mata da mata, ta gabatar da jawabi.
- An Zartas Da Sanarwar Beijing Da Tsarin Aiki A Taron FOCAC
- Li Qiang Ya Gana Da Shugaban Kasar Najeriya
Wadanda suka halarci wannan taro sun hada da matayen shugabannin kasashe, da wakilan shugabannin kasashen Afirka 26 dake halartar taron FOCAC na shekarar 2024 a nan birnin Beijing.
Cikin jawabin da ta gabatar, Peng Liyuan ta ce Sin da kasashen Afirka al’ummu ne masu makomar bai daya, kuma matayen sassan biyu sun kafa wata muhimmiyar hulda ta dunkulewa waje guda, da hadin gwiwa, da aiki kafada da kafada, da nuna basira da jajircewa.
Daga nan sai uwar gidan shugaban kasar Sin din ta gabatar da ribar da aka samu cikin shekaru sama da 30, tun bayan fara aiwatar da shirin Sin mai taken “Spring Bud”, wanda ya mayar da hankali ga amfani da ilimi wajen karfafa damar mata ta cimma burikansu na rayuwa, tare da jinjinawa matan Afirka wadanda suka cimma nasarorin rayuwa a ‘yan shekarun baya-bayan nan ta hanyar samun ilimi.
Peng Liyuan ta kara da cewa, a kan tafarkin bunkasa ci gaban ilimin mata, da kara kusantar makoma mai inganci, Sin da kasashen Afirka na da burika iri daya. Ya dace sassan biyu su ci gaba da aiwatar da ruhin kawance, da hadin gwiwar Sin da Afirka, tare da hada karfi da karfe wajen ingiza ci gaban ilimin yara mata da mata a dukkanin sassan kasa da kasa bisa karin daidaito, da hade dukkanin bangarori, da alkibla mai matsayin inganci, da hada karfi wajen ginawa, da cin gajiyar duniya mai kyau tare. (Saminu Alhassan)