Uwargidan shugaban kasar Sin Xi Jinping, kuma jakadiyar hukumar lafiya ta duniya (WHO) kan cututtukan kanjamau da tarin fuka, Peng Liyuan ta yi kira ga karin hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa domin takaita cututtukan 2, tana mai cewa kawar da su na da matukar muhimmanci wajen kare lafiyar jama’a da tabbatar da walwalarsu, tare kuma da inganta samun ci gaba mai dorewa.
Peng Liyuan ta bayyana haka ne jiya, yayin ganawarta da Winnie Byanyima, mataimakiyar sakatare janar na MDD kuma babbar daraktar hadadden shirin MDD kan yaki da cututtukan kanjamau da tarin fuka (UNAIDS), da Jerome Salomon, mataimakin darakta janar na hukumar WHO.
Peng Liyuan ta kuma yi musu bayani kan ayyuka da dabarun kasar Sin na kandagarki da jinyar cututtukan biyu. Ta kuma bayyana kudurinta na ci gaba da sauke nauyin da ya rataya a wuyanta a matsayinta na jakadiya, tare da bayar da karin gudunmawa ga kokarin duniya na kandagarki da jinyar cututtukan kanjamau da tarin fuka. (Fa’iza Mustapha)