A kwanan baya, Madam Peng Liyuan, Jakadiyar karfafa yaki da cututtukan tarin-fuka da HIV/AIDS ta Kungiyar Kiwon Lafiya ta Duniya (WHO), ta halarci wani gangamin wayar da kai a kan rigakafin AIDS a Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Beijing gabanin zuwan ranar cutar AIDS ta duniya ta shekarar 2024.
A yayin gangamin, ta mika tuta ga wakilin dalibai masu aikin sa-kai na rigakafin cutar AIDS tare da kara masu kwarin gwiwar ci gaba da kyakkyawan aikin da suke yi na kara wayar da kai a kan cutar ta AIDS.
- Matar Da Ta Fi Amfanar Da Al’umma A Shekarar 2024: Olori Atuwatse III
- Hukumar Gwamnati Mafi Ƙwazo A Shekarar 2024: Hukumar Ilimin Bai-ɗaya (UBEC)
Gangamin ya nuna irin ci gaban da aka samu da abubuwan da kasar Sin ta cimma a kan rigakafin cutar AIDS a cikin gida, da kuma karin haske a kan muhimman nasarorin da aka samu a shekarun baya. Ta hanyar cudanyar da aka yi daban-daban ciki har da tattaunawar cikin azuzuwa, wasan kwaikwayo na dandamali da tattaunawa, gangamin ya ilmantar da mahalarta game da hanyoyin rigakafin cutar AIDS da kuma baje kolin ayyukan sa-kai a jami’o’i.
Peng ta yi kira ga dalibai da su kara nuna kuzari da himma wajen yaki da cutar AIDS, tana mai bayyana muhimmancin shigar da matasa cikin wayar da kan jama’a da ilmantarwa a kan rigakafin kamuwa da cutar a rassa da harabobin jami’o’i.
Kafin gangamin dai, sai da Peng ta ziyarci wani baje koli da ya yi bikin cikar kokarin da ake yi na wayar da kai game da cutar HIV/AIDS shekaru goma a jami’o’in yankunan Beijing, Tianjin da kuma Hebei. Hakan ya ba ta damar sanin tasirin da ayyukansu na rigakafi ke yi, da shiga a dama da ita cikin gangamin tare da dalibai da kuma ganawa da malaman kiwon lafiya da masu sa-kai.
Peng ta karfafa gwiwar dalibai su kara hada hannu da aiki tare wajen yaki da AIDS da kuma jaddada bukatar da ake da ita ta nesanta jami’o’i da cutar. (Abdulrazaq Yahuza Jere)