A yau da safe, bisa gayyatar da uwargidan firaministan kasar Thailand Naraporn Chan-ocha ta yi mata, uwargidan shugaban kasar Sin Peng Liyuan, ta ziyarci dakin adana kayan tarihi na fasaha na birnin Ayutthaya tare da abokan zaman shugabanni da wakilai masu halartar taron karba-karba na shugabannin mambobin kungiyar hadin gwiwar tattalin arziki ta Asiya da yankin tekun Pasifik wato APEC karo na 29.
An kafa dakin adana kayan tarihi na fasahar ne bisa ra’ayin mahaifiyar sarkin kasar Thailand Sirikit Kitiyakara, don yada fasahohin hannu na gargajiya na kasar, da kuma taimakawa matalauta a yankunan karkara samun kudin shiga da kansu.
Peng Liyuan ta yabawa wannan batu, inda ta ce lamarin ya yi kama da yadda kasar Sin take yaki da talauci a yankunan karkara masu fama da talauci na kasar.
Yayin da ta ga kayayyakin da yaran da suka bar makaranta, wadanda samu horo a makarantar koyon fasahohin hannu ta gidan sarkin kasar suka samar, Peng Liyuan ta bayyana cewa, za ta sayi wasu kayayyakin don goyon bayan aikin taimakawa matalauta da gidan sarkin kasar Thailand ke gudanarwa. (Zainab)