Ƙungiyar ma’aikatan man fetur da iskar gas (PENGASSAN) ta musanta cewa ta rattaɓa hannu kan yarjejeniyar da aka ce ta kawo ƙarshen yajin aikin da ta shiga kan rikicinta da Matatar Man Dangote. Shugaban ƙungiyar, Festus Osifo, ya ce babban abin da suke nema shi ne a dawo da sama da ma’aikata 800 da aka kora, ba wai batun kuɗin ƙungiya ba.
Osifo ya yi watsi da zargin da kamfanin Dangote ya yi cewa ma’aikatan da aka sallama sun yi ƙoƙarin yi wa matatar zagon ƙasa, yana mai cewa wannan iƙirarin “ba gaskiya ba ne kuma yana da illa ga makomar su.” Ya gargaɗi cewa idan ba a dawo da ma’aikatan ba kamar yadda aka yi alƙawari ba, ƙungiyar na iya dawo da yajin aikin ba tare da wani gargadi ba.
- PENGASSAN Ta Dakatar Da Yajin Aikin Da Ta Fara
- NNPCL Ya Ƙulla Sabuwar Yarjejeniya Ta Samar Da Ɗanyen Mai Na Shekaru Biyu Da Matatar Dangote
Ministan ƙwadago, Mohammed Dingyadi, ya bayyana cewa gwamnati ta matsa lamba har Dangote ya amince da sake ɗaukar ma’aikatan da aka sallama a wasu kamfanonin rukunin Dangote ba tare da asarar albashinsu ba. Ya kuma tabbatar da cewa duk wani ma’aikaci na da ‘yancin shiga ƙungiyar ƙwadago.
Sai dai Osifo ya ce akwai “ruɗani” a yarjejeniyar da aka cimma, ya kuma soki yadda wasu kafafen yaɗa labarai suka damalmala batun. Ƙungiyar TUC ta nuna goyon bayanta ga PENGASSAN, tana mai gargadin cewa ba za a bar kowace ƙungiya ko Kamfani ta tauye haƙƙin ma’aikata ba.
Matatar Dangote ta kare kanta, tana mai cewa sake tsarinta wajibi ne don tsaro da inganci, tare da zargin PENGASSAN da amfani da dabaru marasa dacewa. A halin yanzu, kotun masana’antu ta bayar da umarnin dakatar da ci gaba da yajin aikin har zuwa zaman sauraron ƙarar a ranar 13 ga Oktoba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp