Ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar Labour Party (LP), Peter Obi, ya zaɓi Doyin Okupe a matsayin mataimakinsa na riƙo kafin ya gama shawarar wanda zai zaɓa.
Jam’iyyar LP ta miƙa wa INEC sunan Doyin Okupe a daidai lokacin da wa’adin da hukumar zaben ta bai wa jam’iyyu ke dab da ƙarewa a daren yau Juma’a.
An haifi Doyin Okupe, a Adedoyin Ajibike Okupe, ranar 22, ga Watan Maris 1952, Karamar hukumar Iperu, Jihar Ogun.
Okupe l, shi ne tsohon mai tamaka wa tsohon Shugaban Ƙasa Goodluck Jonathan kan kafofin yaɗa labarai.
“Yanzu haka da nake magana da ku, ni nake riƙe da mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour Party,” a cewar Okupe yayin da ya bayyana ta cikin shirin Politics Today na kafar talabijin ta Channels TV a yau Juma’a.
Okupe ya tabbatar da cewa Mista Obi na ci gaba da shawarwari game da wanda zai zaɓa a matsayin abokin takarar tasa.
Hukumar ta saka yau Juma’a 17 a matsayin rana ta ƙarshe da jam’iyyu za su miƙa mata sunayen ‘yan takarar da suka zaɓa da za su wakilce su a zaɓen 2023, amma suna iya sauya sunayen mataimakan ‘yan takarar.