Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party, (LP), Peter Obi, ya mayar da martani game da mummunan harin da wasu da ake zargin ‘yan daba ne suka kai wa magoya bayansa a Jihar Legas.
Obi yayi Allah wadai da duk wani nau’in tashin hankali da ‘yan daba na siyasa da kuma hare-haren da ake kai wa magoya bayan nasa.
- Mun Shirya Wa Masu Fizgen Na’urar Tantance Rajistar Zaɓe – INEC
- Duk Wanda Zai Yi Noma Ya Tabbatar Da Kiyaye Lokaci – AFAN
Leadership Hausa ta ruwaito harin da aka kai wa magoya bayan Obi a Legas.
Idan za a tuna cewa jam’iyyar LP, ta gudanar da yakin neman zaben shugaban kasa a Legas ranar Asabar.
Bayanin nasa na kunshe ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Asabar.
Obi ya yi kira ga jami’an tsaro a fadin kasar nan da su kare wadanda suke amfani da ‘yancin fadin albarkacin baki da taro.
Ya ce, “Yayin da muka shiga matakin karshe na zaben 2023, ina kira ga ‘yan Nijeriya ba tare da la’akari da siyasa ko ra’ayi ba, da su guji tashin hankali. Ina Allah wadai da duk wani nau’i na tashin hankali da ‘yan daba na siyasa; musamman hare-haren da ake kai wa magoya bayana masu biyayya.
“Ina kira ga jami’an tsaro a fadin kasar nan da su kare wadanda suke amfani da ‘yancin fadin albarkacin baki da taro. Bai kamata ake kai wa mutanen da ba su ji ba su gani ba hari.”
Sai dai magoya bayan Obi, sun zargi jam’iyyar APC mai mulki da daukar nauyin harin da aka kai musu.