Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour (LP) a 2023 kuma tsohon gwamnan Jihar Anambra, Peter Obi, ya kai ziyara Jihar Bauchi a ranar Alhamis don wata ganawa ta musamman.
Da isarsa filin jirgin sama na Sir Abubakar Tafawa Balewa, Mataimakin Gwamnan Jihar Bauchi, Rt. Hon. Mohammed Auwal Jatau, ne ya tarɓe shi. Obi ya ziyarci Gwamna Bala Mohammed a fadar gwamnati, inda suka yi wata ganawar sirri.
- Matashi Ya Kashe Mahaifiyarsa Da Taɓarya A Bauchi
- Gwarzon Ɗan Kasuwa Na Shekarar 2024: Benedict Peters
Duk da cewa dalilin ziyarar bai fito fili ba, ana hasashen cewa yana da alaƙa da shirin siyasar 2027, inda ake ta raɗe-raɗin haɗakar ‘yan adawa domin ƙalubalantar jam’iyyar APC mai mulki.
Taron ya ƙara hura wutar jita-jitar haɗakar jam’iyyun adawa, musamman bayan ganawar da Atiku Abubakar ke yi da manyan ‘yan siyasa irin su Obi da kuma tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp