Peter Obi, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour a zaben 2023, ya ziyarci jihar Kano domin duba waɗanda gobarar wani masallaci ya rutsa da su a asibitin ƙwararru na Murtala Muhammad. Ya nuna baƙin cikinsa tare da yin Allah wadai da wannan ta’addancin.
Obi ya jaddada muhimmancin haɗin kai da tallafawa waɗanda abin ya shafa da ma’aikatan asibitin. Ya ce ya kai ziyarar ne domin nuna goyon baya da kuma yin Allah wadai da wannan ta’addancin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane 11.
- Hisbah Ta Haramtawa Maza Masu Kiɗan DJ Shiga Wurin Shagalin Bikin Mata A Jihar Kano
- Ƙananan Hukumomin Kano 14 Na Fuskantar Barazanar Ambaliyar Ruwan Sama — NiMET
Gobarar ta afku ne a Larabar-Albasawa a ƙaramar hukumar Gezawa ta jihar Kano a lokacin da Shafiu Abubakar ya cinnawa wani masallaci wuta a lokacin sallar asuba, inda lamarin ya rutsa da mutane kusan 40 a ciki. Shafi’u ya yi hakan ne domin fusata kan zargin rashin adalcin da aka yi masa a rabon gado.
Obi ya jajanta wa gwamnati da al’ummar jihar Kano, inda ya buƙaci ƴan Najeriya da su haɗa kai don daƙile irin wannan tashin hankalin. Ya yi Allah-wadai da wannan aika-aika tare da yin alƙawarin tallafa wa waɗanda abin ya shafa.