Kakakin watsa labaran rundunar sojojin ‘yantar da al’ummar kasar Sin wato PLA dake yankin gabashin kasar Shi Yi ya bayyana cewa, rundunar za ta gudanar da sintiri da atisayen soja na gargadi a kewayen tsibirin Taiwan tsakanin yau 8 zuwa 10 ga wannan wata, domin share fagen yaki. Matakin na zama wani gargadi mai tsanani ga talakan da masu neman ‘yancin kan Taiwan suke yi tare da rukunonin ketare, kuma matakin ya zama wajibi domin kare ikon mulkin kasar da cikakken yankinta.
Kakakin ya kara da cewa, rundunar sojojin kasar Sin za ta gudanar da sintiri da atisayen soja na gargadi a zirin Taiwan da arewaci da kudanci da kuma gabashin tsibirin na Taiwan bisa shirin da aka tsara. (Mai fassarawa: Jamila)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp