Jam’iyyar PRP ta tabbatar da cewa ta fara tattaunawa da wata jam’iyyar adawa ta ADC, kan yuwuwar hadewar jam’iyyun gabanin babban zaben shekarar 2027.
Shugaban jam’iyyar PRP na kasa, Falalu Bello ne ya bayyana hakan a wani taron hadin gwiwa da takwaransa na ADC, Ralph Nwosu a Abuja.
- Da Rancen Naira Tiriliyan 13 Za A Cike Gibin Kasafin Kudin 2025 — Edun
- Kisan Jami’an ‘Yansanda 229 A Cikin Wata 22 Babbar Musiba Ce Ga Kasa
Matakin na zuwa ne kwanaki uku bayan da jam’iyyar APC mai mulki ta yi gargadin cewa babu wani hadewar shugabannin ‘yan adawa da suka hada da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar da tsohon gwamnan Anambra, Peter Obi, da zai iya kwace kujerar Shugaban kasa Bola Tinubu a zaben 2027.
Jam’iyyar APC na mayar da martani ne kan kalaman da mai magana da yawun Atiku, Paul Ibe, ya yi cewa shugaban nasa da takwaransa na jam’iyyar LP duk sun koyi darasi a zaben da ya gabata, kuma za su hada kai domin korar jam’iyya APC a kan karagar mulki.
Haka zalika, wasu jam’iyyun siyasa na adawa a karkashin inuwar hadakar jam’iyyun siyasa da jam’iyyar SDP, su ma sun bayyana shirinsu na tattaunawa kan yiwuwar yin kawance, suna masu cewa kasar na bukatar hadakar Atiku da Obi.
Da yake yi wa manema labarai jawabi a ranar Juma’a, Bello ya tabbatar da cewa tuni suka fara tattaunawa da shugabannin ADC domin fara shirin ceto kasar nan daga hannun jam’iyya mai mulki.
Ya ce, “Eh, mun fara tattaunawa. Ba ma tsoron hadewa gaba daya. Mu duba tarihin zabe. PRP ita ce jam’iyyar siyasa mafi tsufa a yau. Mun kafa gwamnati a Kaduna a shekarar 1979, saboda kawancen siyasa da jam’iyyun UPN, NPP, da PNP a jihar.
“Idan sauran jam’iyyu suna son shiga cikinmu, to muna maraba da su. Kofofinmu a bude suke ga kowa da kowa hatta daidaikun mutane, ba jam’iyyun siyasa kadai ba. Amma idan sun gwammace su shiga jam’iyyar da ba ta son jama’a da maganar kudi kawai, su koma PDP da APC. Abin da suka tsaya a kai kenan.
“Don haka muna cewa mun gaji kuma muna son wani sabon sauyi. Idan kuma hakan ya bukaci ni ko shugaban jam’iyyar ADC ya sauka daga mukaminsa, to haka ya kasance. Wannan kasa ta fi mu muhimmanci. Kundin tsarin mulkin jam’iyyar PRP yana wakiltar ka’ida da akidar da muke tsayawa a kai.”
Nwosu ya kuma ce bukatar a hada kai ta kara samun karbuwa sakamakon gano cewa suna da akida daya.
Shugaban jam’iyyar ADC ya bayyana cewa, a halin da ake ciki wahalhalun da ake fama da su a kasar nan bai kamata a ce jama’a sun gaji ba, kuma suna bukatar sabon sauyi.
“Hadin kai da hadin gwiwa wanda a karshe zai haifar da yuwuwar hadaka yana gudana tsakanin PRP da ADC. Me ya sa muke yin haka? gina akidar siyasa da fayyace hangen inda muka dosa.
“Jam’iyyunmu ne suka fara wannan magana ta kawance, ba wai ta mutanen da ke neman mukami ba ne. Wadannan shugabannin jam’iyyun siyasa ne wadanda suke jin cewa ya kamata a samu sauyi a kasar nan kuma suna son ci gaba. A karshe, idan mutanen da ke neman mukami sun shigo dole ne su bi wasu ka’idojin da ya kamata su bi. Damuwarmu game da dimokuradiyya a fili take,” ya kara da cewa.