Hukumar kula da harkokin ‘yansanda ta kasa (PSC), a ranar Laraba ta amince da korar ‘yansanda uku masu mukamin mataimakan Sufuritendan (ASPs) sannan, ta kuma rage mukamin mai taimakawa kwamishina (ACP), babban Sufuritendan, wasu jami’ai biyu masu mukamin Sufuritendan da wani mataimakin Sufuritendan bisa kama su da laifuka daban-daban da suka hada da rashin da’a/ladabi da biyayya hadi da wasu laifukan.
Hukumar ta kuma amince da tsawatarwa/gargadi mai tsanani ga wani mataimakin kwamishinan ‘yansanda, babban Sufuritenda, da Sufuritenda su hudu, da wasu mataimakan Sufuritendan (DSP) su biyu hadi da masu taimaka wa Sufuritendan ‘yansanda su 12 (ASPs).
Hukumar ta cimma wannan matsayar ne a zamanta karo na 20 da ya gudana a ranar Laraba a shalkwatar hukumar da ke Jabi, Abuja wanda shugaban hukumar kuma tsohon Sufeto-janar na ‘yansanda, Dakta Solomon Arase ya jagoranta.
Kakakin hukumar, Ikechukwu Ani, a sanarwar da ya fitar ranar Laraba da daddare, ya shaida cewar hukumar ta kuma amince da hukuncin gargadi mai tsauri ga wasu jami’ai shida da Sufuritenda daya da mataimakan Sufuritendan guda biyar.
Kazalika, hukumar ta kuma amince da karin girma ga wasu manyan jami’an hukumar su 109.
Shugaban hukumar wanda a karonsa na farko ke nan ya jagoranci zaman hukumar tun bayan nada shi da shugaba Buhari ya yi, ya taya sabbin jami’an da suka samu karin girman murna, sai ya kalubalancesu da su kari ninka kokarinsa domin sauke nauyin da ke rataye a wuyayensu wajen gudanar da aiki yadda ya dace.
Dr. Arase ya ce, dole ne su tashi tsaye su kara azama da himma domin kyautata aikin hukumar PSC.
Ya bada tabbacin cewa karin girma ga Jami’ai na daga cikin muhimman abubuwan da zai sanya a gaba, amma fa sai ya ce dole ne sai kowani jami’i zai ji cewa a shirye yake ya kara kokari wajen sauke nauyin da ke kansa.
Kazalika, shugaban na PSC ya nemi ‘yansanda da a kowani lokaci suke gudanar da ayyukansu biya tafiya kan ka’idar da dokokin da aka gindaya domin kyautata aikinsu.
Ya ce, matakin ladabtarwa zai sauka kan duk jami’an da aka kama da aikata laifuka kuma a hukuntasu daidai da laifukansu domin cigaba da tsarkake bangaren aiki da tabbatar da aikin dan sanda na tafiya bisa kwarewa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp