Kungiyar kwallon kafa ta Paris St-Germain na iya neman sayen dan wasan gaban Napoli Bictor Osimhen, mai shekara 24 domin maye gurbin Kylian Mbappe wanda ake tunanin kungiyar za ta sayar da shi kafin kwantaraginsa ya kare a shekara mai zuwa.
Mbappe ya fito fili ya bayyana aniyarsa ta barin PSG a kyauta idan kwantaraginsa ya kare a watan Yunin shekara ta 2024, sai dai PSG na da burin sayar da shi a wannan bazarar idan har bai sanya hannu kan sabon kwantaragi da kungiyar ba.
- Jihohin Da Aka Samu Mahajjata Masu Juna Biyu Za Su Fuskanci Hukunci – NAHCON
- Yarjejeniyar Saukaka Zuba Jari Za Ta Bunkasa Tattalin Arzikin Duniya Da Dala Triliyan 1
Rahotanni sun tabbatar da cewa dan wasan na Nijeriya ne zai zama kan gaba cikin wadanda PSG za ta yi zawarci domin maye gurbin Mbappe idan cinikin Mbappe ya kankama a bazaran nan, hakan zai kara nauyin aljihun PSG, wanda zai iya ba su damar biyan bukatun da Napoli za su yi kan Osimhen.
Duk da sha’awar da PSG ke yi, Napoli na sa ran cewa za ta iya tsawaita kwantiragin Osimhen amma idan har Osimhen zai sauya kungiya mai yiwuwa ya kai kusan fam miliyan 130, kodayake kwanan nan ya yi ikirarin bai damu ba ko ya zauna a Napoli ba ko a’a.