Kungiyar kwallon kafa ta PSG ta sallami Mauricio Pochettino daga mukaminsa na horar da ‘yan wasanta bayan shafe watanni 18 a kungiyar.
PSG ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da Ta fitar tana mai cewa: “Paris Saint-Germain ta tabbatar da cewa ta kawo karshen kwantiraginta da Mauricio Pochettino.”
“Kungiyar tana gode wa Mauricio Pochettino da ma’aikatansa kan kokarin da suka yi a tsawon lokacinsu a Kungiyar suna horar da ‘yan wasanta, kungiyar tana musu fatan alheri a rayuwarsu tana nan gaba.”
Kungiyar ta Faransa ta maye gurbin Pochettino da Christophe Galtier.