ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Sharhi: Laifin Wani Ba Ya Shafar Al’umma Duka

by CMG Hausa
4 years ago
Sharhi

Xiaozhong Johnny wani mai wallafa bidiyo ne a shafin sada zumunta, wanda ya dan yi suna a kasar Sin.

Xiaozhong ya fara zuwa Afirka ne sama da shekaru biyu da suka wuce, kafin daga bisani ya zauna a birnin Lome, babban birnin kasar Togo. Kamar yadda matasan yanzu suke yi, Xiaozhong shi ma ya kan dauki hotunan bidiyo iri na “Vlog” bisa ga harkokin rayuwarsa na yau da kullum a Afirka, sa’an nan ya wallafa su a shafukan sada zumunta bisa sunan Xiaozhong Johnny, sai dai bai yi zaton hakan zai sa ya samu dimbin masu bibiyarsa ba.

  • Sin Tana Maraba Da Kasa Da Kasa Su Shiga Kiran Raya Duniya

Cikin shekarun biyu da suka wuce, Xiaozhong ya ziyarci kasashen Afirka 13, tare da wallafa hotunan bidiyo sama da 300, lamarin da ya sa ya samu masu bibiyarsa kusan miliyan a shafukan sada zumunta.

ADVERTISEMENT

Wasu sun ce sun yi farin ciki da samun damar bin sawun Xiaozhong ziyartar kasashen Afirka ba tare da fita daga gida ba. Wadannan hotunan bidiyo da Xiaozhong ya wallafa, sun kuma sa masu bibiyarsa sun samu damar kara fahimtar hakikanin yanayin da ake ciki a Afirka daga dukkan fannoni, musamman ma sun taimaka wajen gyara wasu kura-kuran da a baya suka samu wajen fahimtar nahiyar.

Xiaozhong ya ce, “Na je Cote d’Ivoire, na je Gabon, kuma ta hoton bidiyon da na wallafa, masu bibiyarmu sun gano cewa, lallai akwai hanyoyi da gine-gine masu kyau a wurin, kuma al’umma na jin dadin rayuwarsu, sun kuma tambaye ni, da gaske nan Afirka ne? Ina ganin bidiyon da na wallafa sun kawo gyara ga ra’ayoyinsu.”

LABARAI MASU NASABA

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

Ya zuwa karshen bara, shekaru 12 a jere ne kasar Sin ta kasance ta farko wajen yawan yin ciniki da kasashen Afirka, baya ga haka, Afirka ta zama ta biyu ga kasar Sin wajen yawan samar da kwangilar gine-gine.

Dimbinayyukan more rayuwa da kasar Sin ta aiwatar a kasashen Afirka, sun taimaka wajen inganta yanayin ayyukan more rayuwa, da ma rayuwar al’ummar kasashen. Daga cikin masu bibiyar malam Xiaozhong, akwai wasu da ke kiran shi “manzon Sin da Afirka”.

Hakika abun haka yake, a yayin da huldar tattalin arziki da ciniki ke kara karfafa a tsakanin Sin da Afirka, al’ummar sassan biyu ma na kara cudanya da juna, bisa ga taimakon da irinsu Xiaozhong suka bayar, al’ummar sassan biyu na kara fahimtar juna da kuma amincewa da juna.

A hakika, irinsu Xiaozhong da ke rayuwa a Afirka, tare da wallafa bidiyo game da rayuwarsu a Afirka suna da yawa, kuma ta bidiyon da suke wallafawa, karin Sinawa na samun damar fahimtar al’ummar kasashen Afirka, da al’adunsu, da bunkasuwar tattalin arziki, da zaman al’umma na kasashen, baya ga kuma yadda hakan ya taimaka wajen hada zukatansu, duk da nisan da ke tsakaninsu da ma bambancin al’adunsu.

Amma abun bakin ciki shi ne, akwai ‘yan tsirarun mutane da suka dauki hotunan bidiyon da ba su dace ba, tare da wallafa su a shafukan sada zumunta. Ga misali a kwanan baya, an kama wani dan kasar Sin da ke rayuwa a Malawi, wanda ya wallafa bidiyon da ake ganin yana nuna kabilanci.

A game da lamarin, bi da bi, ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, da ma ofishin jakadancin kasar da ke Malawi, sun yi Allah wadai da abun da ya yi, kuma shugaban sashen kula da harkokin Afirka na ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mr. Wu Peng, shi ma ya bayyana cewa, har kullum kasar Sin na nuna rashin amincewa da nuna kabilanci, kana kasar za ta ci gaba da dakile abubuwan da ke baza ra’ayin kabilanci a shafukan sada zumunta.

A game da lamarin, ya kamata mu gane cewa, a duk kasashe da shiyyoyi, akwai mutane masu kirki da ma marasa kirki, amma marasa kirki ‘yan tsiraru ne, wadanda ba sa wakiltar wata kasa, ko al’ummarta baki daya ba.

Sin da kasashen Afirka na da dadadden zumunci, kuma nasarorin da aka cimma bisa hadin gwiwar sassan biyu ta fannoni daban daban ba su da sauki, don haka, ya kamata mu darajanta su. “Kada dai mu bari wake daya ya bata miya”, balle ma a ce a bari wasu su yi amfani da waken wajen cimma yunkurinsu na musamman. (Lubabatu)

Sharhi
CMG Hausa
+ postsBio
  • CMG Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cmg-hausa/
    Shugabannin Kasashen Duniya Sun Yi Wa Sin Fatan Alheri A Sabuwar Shekara
  • CMG Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cmg-hausa/
    San Francisco sabon mafarin hadin gwiwar Sin da Amurka ne
  • CMG Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cmg-hausa/
    Xi Ya Halarci Kwaya-Kwaryan Taron Shugabannin Mambobin APEC
  • CMG Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cmg-hausa/
    Shugaban Kasar Sin Ya Gabatar Da Rubutaccen Jawabi Ga Taron Jagororin Masana’antu Da Kasuwanci Na APEC

MASU ALAKA

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna
Daga Birnin Sin

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

September 9, 2026
Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba
Daga Birnin Sin

Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

September 9, 2026
Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa
Daga Birnin Sin

Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

September 9, 2026
Next Post
Kyautata Dangantaka Da Sin Na Iya Taimakawa Amurka Shawo Kan Matsalar Tattalin Arzikin

Kyautata Dangantaka Da Sin Na Iya Taimakawa Amurka Shawo Kan Matsalar Tattalin Arzikin

LABARAI MASU NASABA

Gwamna Yusuf Ya Umarci Jami’an Tsaro Su Gano Waɗanda Suka Kashe Danshagamu

September 10, 2026
Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

September 9, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

September 9, 2026
Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

September 9, 2026
Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

September 9, 2026
Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

September 9, 2026
Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

September 9, 2026
Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

September 9, 2026
“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

September 9, 2026
’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja

’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja

September 9, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.