A yayin zantawarsa da ’yar jaridar Babban Gidan Rediyo da Talabijin na kasar Sin wato CMG, firaministan kasar Nepal Pushpa Kamal Dahal, ya bayyana cewa, ya yi farin ciki sosai da halartarsa bikin bude gasar wasannin Asiya, kasancewar a yayin bikin, ya zanta da shugaban kasar Sin Xi Jinping, game da hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu.
A cewarsa, ’yan wasannin motsa jiki na kasar Nepal sun halarci gasar wasannin Asiya cikin himma da kwazo, tun daga gasar ta karon farko. Kuma a wannan karo ma kasar Nepal ta tura ’yan wasannin motsa jiki sama da dari 2 zuwa kasar Sin domin halartar gasar.
Kasancewar gasar na da muhimmanci sosai ga ’yan wasanni, da al’ummomin kasar Nepal, har ma da shi kansa. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp