Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin a jiya Laraba ya gana da mamban ofishin siyasa na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin kana darektan ofishin hukumar kula da harkokin waje ta kwamitin kolin, a birnin Moscow, babban birnin kasar ta Rasha.
A yayin ganawar, Mr. Wang Yi ya ce, ba domin wani bangare na uku ne Sin da Rasha ke bunkasa huldar da ke tsakaninsu a sabon zamanin da ake ciki ba, haka kuma duk wani bangare na uku ba zai iya haifar da tasirinsa a kan huldar ba, ballantana a ce ya haifar da barazana. Kasar Sin na son hadin kai da Rasha, su karfafa amincewa da juna ta fannin siyasa da ma inganta hadin gwiwa ta fannin tsare-tsare, tare kuma da fadada hakikanin hadin gwiwa a tsakaninsu, don kiyaye halastacciyar moriyarsu, da kuma taka rawar da ta dace ta fannin kiyaye zaman lafiya da ci gaba na duniya.
Shugaba Putin a nasa bangaren ya ce, yanzu haka huldar dake tsakanin kasashen biyu na bunkasa kamar yadda ake fatan gani, inda kasashen biyu suka cimma gaggaruman nasarori a hadin gwiwar da ke tsakaninsu ta fannoni daban daban da ma cikin kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai da kuma kungiyar BRICS, baya ga kuma yadda suka inganta hadin kai a cikin al’amuran duniya, wanda hakan ke da muhimmiyar ma’ana wajen kiyaye dimokuradiyya a huldar kasa da kasa da kuma daidaito a tsarin kasa da kasa.
Kasashen biyu sun kuma yi musayar ra’ayoyi a kan batun Ukraine, inda Wang Yi ya yaba da yadda Rasha din ta nanata niyyarta ta daidaita batun ta hanyar yin shawarwari.
Wang Yi ya ce, kasar Sin za ta ci gaba da tsayawa a kan matsayin adalci, don ba da gudummawa ta fannin daidaita batun a siyasance. (Lubabatu Lei)