Magoya bayan tawagar Morocco da ke fatan zuwa kallon wasan kasar da Faransa a ranar Laraba, sun fuskanci É“acin rana, yayin da aka soke wasu jiragen da ya kamata su yi jigilarsu da kuma matsalar É“acewar tikitin jirgi.
BBC ta rawaito cewa, Kamfanin jirgin kasar – Royal Air Moroc, ya soke tashin jirage bakwai a yau, yana mai É—ora laifin ga hukumomin Qatar.
- Qatar 2022: Argentina Ta Je Matakin Wasan Karshe
- Qatar 2022: Morocco Ta Kara Bada Jirage 30 Don Jigilar Magoya Bayanta Zuwa Qatar
Wasu ƴan ƙasar da suka riga suka isa Qatar sun ce babu tabbas kan dubban tikitin da hukumar ƙwallon Morocco ta yi alƙawari.
Morocco dai ta kasance ƙasa ta farko daga Afrika, kuma ta farko daga ƙasar Larabawa da ta kai zagayen dab da ƙarshe a gasar cin kofin duniya da ke gudana a Qatar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp