A babban taron hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA karo na 70, wanda aka yi a watan Satumbar shekara ta 2020, mambobin hukumar sun amince da wani canji na damar buga wa kasashe wasa.
Sai dai kafin wannan lokacin, doka ta bayyana cewa duk dan wasan da ya bugawa kasa wasa guda daya ba zai sake zuwa wata kasar ya buga mata wasa ba har karshen rayuwar sa wanda a haka aka dade ana tafiya.
Sai dai a babban taron na FIFA karo na 70, an amince cewa idan dan wasa ya buga wasa daya zai iya canja kasar da yake so a gaba har sai idan wasa uku ya buga, hakan yana nufin idan dan wasa ya buga wa kasa wasa uku na wata gasar ba shi da damar zuwa wata kasar ya buga mata wasa.
A gasar cin kofin duniyar da a yanzu haka ake ci gaba da fafata wa a kasar Qatar, akwai ‘yan wasa da dama daga nahiyar Afirka da suke buga wa kasashen da bana Afirka ba:
Dan wasa Musab Kheder: Dan wasan baya, yana buga wa kasar Qatar wasa ne sai dai a birnin Khartoum na kasar Sudan aka haife shi kuma yana buga wasanninsa a kungiyar Al-Sadd ta kasar Qatar.
Ansu Fati: Shima zakakurin dan wasa ne wanda yake wakiltar tawagar ‘yan wasan kasar Spaniya sai dai an haife shi ne a kasar Guinea-Bissau kafin ya koma kasar Spain tun yana dan karamin yaro.
Alphonso Dabies: Matashin dan wasa wanda yake buga wasan sa a kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munchen ta kasar Jamus, dan wasan mai shekara 22 a duniya, yana buga wasa a tawagar kasar Canada amma kuma an haife shi ne a birnin Budurburam na kasar Ghana.
Eduardo Camabinga: Kwararren dan wasa ne wanda yake buga wasa a kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid kuma yana wakiltar kasar Faransa ne amma kuma an haife shi ne a sansanin ‘yan gudun hijira na Angola bayan da iyayensa suka gudu daga kasar Congo amma kuma ya girma a Faransa.
Youssoufa Moukoko: Dan wasa ne wanda yake buga wasa a kungiyar kwallon kafa ta Borrusia Dortmund dake kasar Jamus amma kuma an haife shi ne a babban birnin kasar Kamaru wato Yaounde kuma kawo yanzu yana da shekara 18 a duniya.
Danilo Pereeira: Dan wasan na kungiyar kwallon kafa ta Paris Saint German mai shekara 31 a duniya yana wakiltar kasar Portugal ne a wasannin kasashe amma kuma a kasar Guinea-Bissau aka haife shi.
Stebe Mandanda: Mai tsaron ragar kungiyar kwallon kafa ta Rennes ta kasar Faransa yana wakiltar tawagar ‘yan wasan kasar ta Faransa ne amma kuma an haife shi ne a Jamhuriyar Dimokradiyar Congo.
Breel Embolo: Dan wasan da a yanzu yake wakiltar kasar Switzerland a wasannin kasa da kasa kuma yana buga wa kungiyar kwallon kafa ta Monaco ta kasar Faransa, an haife shi a babban birnin kasar Kamaru wato Yaounde.
Mohammed Muntari: Mai shekara 28 a duniya an haife shi ne a kasar Ghana amma kuma yana buga wasa a tawagar ‘yan wasan kasar Qatar tare da kungiyar kwallon kafa ta Al-Duhail dake Qatar.
Amadou Onana: Dan wasan mai shekara 28 a duniya an haife shi ne a babban birnin kasar Senegal wato Dakar amma yanzu yana wakiltar tawagar ‘yan wasan kasar Belgium ne a wasannin kasa da kasa kuma yana buga wasa a kungiyar kwallon kafa ta Eberton ta kasar Ingila.
William Cavalho: Dan wasan yana buga wasa a kungiyar kwallon kafa ta Real Betis ta kasar Spain kuma yana wakiltar tawagar ‘yan wasan kasar Portugal ne a wasannin kasa da kasa amma kuma a kasar Angola aka haife shi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp