Ministan wajen Sin Qin Gang ya tattauna ta wayar taho da takwaransa na Zambiya Stanley Kasongo Kakubo a jiya Litinin.
Qin Gang ya bayyana cewa, Sin da Zambiya abokai ne “a ko da yaushe”. Bangaren Sin yana son karfafa hadin gwiwa mai ma’ana a dukkan fannoni wajen neman ci gaba mai inganci bisa shawarar “Ziri daya da hanya daya” da dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka, wato FOCAC. Haka kuma kasar Sin na maraba da shigowar karin kayayyakin Zambiya masu inganci zuwa kasuwanni kasar Sin.
Qin Gang ya kara da cewa, kamata ya yi Sin da Zambiya su karfafa hadin gwiwa a kan batutuwan kasa da kasa da na shiyya-shiyya, da kuma nuna adawa da ra’ayin bangare daya da ba da kariya da kuma ayyukan nuna karfin tuwo, ta yadda za a kare moriyar kasashen biyu da ta sauran kasashe masu tasowa.
A nasa jawabin Kakubo ya nuna godiya ga goyon bayan da bangaren Sin ya dade yana baiwa Zambiya, wajen neman ci gaban kasar. Yana fatan sassan biyu za su ci gaba da karfafa hadin gwiwa a tsakanin su a fannoni daban daban, a kokarin inganta huldar abokantaka a ko da yaushe tsakanin kasashen biyu.
Dadin dadawa, Mr. Kakubo ya nanata cewa, bangaren Zambiya yana martaba manufar kasar Sin daya tak a duniya, yana kuma fatan za su kara goyon bayan juna a kan batutuwan dake shafar moriyarsu da kuma muhimman batutuwan dake shafarsu. (Safiyah Ma)