Kamar dai yadda ya saba a duk farkon shekara mai kamawa, a ranar A Asabar din karshen makon jiya ma, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da jawabi, mai kunshe da sakon gaisuwa, da taya murna ga daukacin al’ummar duniya bisa shigowar sabuwar shekarar 2023.
Shugaba Xi ya bayyana cewa, kasar Sin ta yanzu, tana da kusanci sosai da sauran sassan duniya, wanda hakan ke nuna karsashinta, da karko, wanda zai ba ta damar ingiza daidaito da tabbaci ga ci gaban duniya baki daya.
Sakamakon wasu alkaluman jin ra’ayin jama’a da aka fitar a baya bayan nan, ya nuna kaso 78.34 bisa dari na al’ummun duniya na da imanin cewa, tattalin arzikin duniya ya zama tamkar injin dake ingiza tattalin arzikin duniya, suna kuma fatan tattalin arzikin kasar zai taka sabuwar rawar gani.
Tawagar kwararru ta CGTN, da cibiyar jin ra’ayin al’umma ta jami’ar Renmin ta kasar Sin ne suka jagoranci tattara ra’ayin na al’ummun kasa da kasa, inda suka gano cewa, al’ummun kasashe da yankuna 41, dake wakiltar kaso 65.2 bisa dari na jimillar al’ummar duniya, sun goyi bayan wannan matsaya. (Saminu Alhassan)