Dangane da yadda wasu kasashen yammacin duniya suke yada ra’ayin raguwar tattalin arzikin kasar Sin, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning ta musahanta hakan a gun taron manema labaru da aka gudanar a yau. Ta kuma yi nuni da cewa, har yanzu tattalin arzikin kasar Sin shi ne babban injin da ke kawo ci gaban tattalin arzikin duniya.
Mao Ning ta yi nuni da cewa, tun farkon wannan shekara, farfadowar tattalin arzikin duniya ya yi rauni, kana yanayin duniya yana da sarkakkiya. Amma duk da haka tattalin arzikin kasar Sin yana samun farfadowa, da bunkasuwa yadda ya kamata. A cikin watanni 6 na farko wannan shekarar, yawan GDP na kasar Sin ya karu da kashi 5.5 cikin dari bisa na makamancin lokacin bara. Asusun bada lamuni na duniya wato IMF ya yi hasashen cewa, tattalin arzikin Sin a bana zai karu da kashi 5.2 cikin dari, wanda zai samar da gudummawar kashi 1 cikin kashi 3 ga bunkasuwar tattalin arzikin duniya baki daya.
Ban da wannan kuma, Mao Ning ta mayar da martani ga sanarwar da hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa (IAEA) ta fitar ta sanya ido kan yadda kasar Japan ke zubar ruwan dagwalon nukiliya a cikin teku, tana mai cewa, bincike ko sa ido ba ya nufin ba da izni ga Japan na zubar da ruwan dagwalon nukiliya cikin teku, kuma ba a baiwa kasar Japan ikon gudanar da aikin ba, ya kamata kasar Japan ta hanzarta dakatar da hadarin gurbata muhallin duniya da gurbataccen ruwan nukiliya. (Zainab)