Barkanmu da saduwa a wannan fili na Ra’ayi Riga, wannan mako mun kawo muku ra’ayin masu bibiyarmu ne a kan sabon salo na dan takarar Mataimakin Shugaban Kasa na ‘Wucin-gadi’ da Jami’yyar APC ta tura wa INEC.
Shamsuddeen Ahmad Idris
Ai daman da kai da kaya duk mallakan wuya ne, wannan ba wani abu ba ne, ai kasarma tasu ce, don haka yadda suka ga dama za su yi.
Sani Bello Kano
Ni ban san ma me zan ce ba matsala dai an sameta kasa ta gama rasa jagoranci duk wanda za su kawo sai an ji ya yi wata katobara kuma babu dama talaka ya yi magana basa jin ko wane yare sai zancen kudi
Sannan kuma hakan ya nuna basu ma shirya wa kasar komai ba sai son ransu babu wani tanadin alkhairi, kawai mu dai babu abinda ya kamace mu sai addu’ar Allah ya zaba mana mafi alkhairi
It’z Sam Dambatta
Ai wannan shi yake nuna mana cewa kawai mulkin ake so ayi. Bawai kawo wa kasa mafita ba, mu dai fatan mu Allah ya zaba mana mafi alkhairi
Umar Ibrahim Umar
Allah ya kyauta, wani abu sai Nijeriya wannan shi yake nuna maka cewa tun daga tsarin tsayawa takara babu tsari babu shiri ba a tsara wanda zai yi mataimakin wanda zai yi mataimakin dan takara ba har yanzu, kenan yana nuna koda ace nasara aka yi babu wani shiri kenan a kasa don gudanar da shugabanci nagari, Allah dai Ya taimaka mana, Amin
Omar Naseer Imam
Toh abin dai kam ya zo mana da mamaki, fatanmu shi ne Allah ya bamu shugabanni nagari
Sulaiman Muhammad
To wannan sai lauyoyi
Bashir Ibrahim Matazu
Shi wannan tsarin na aan takarar Mataimaki na wucin-gadi shi ne ke nuna maka cewa ita kanta kasar basu shirya mata komai ba sai dai kawai Allah Ya bamu mafita.
Ibrahim Hassan Baban Adila
Anya wannan jam’iyyar APC ba shiga cikin rudani ba kuwa?, tayaya aka taba yin haka, wannan ya nuna wa mutane suna jin shakkan jam’iyyar PDP kenan kuma sun rasa mafita. Daga karshe Allah ya zaba mana shuwagabanni nagari kuma mafi alkhairi a garemu, Ameen. Ibrahim Hassan Minister Baban Adila da Ansar, Gombe
Rchp Ahmad Shehu Babaldu
Nijeriya kasarmu ta gado!
Yanzu inda ace kasa ce mai doka, kamata ya yi ace wadda suka dauki mataimaka na wucin gadi a hukuntasu daidai da abinda suka aikata tunda sun sabawa dokar zabe ta kasa. Amma abin takaici sai gashi jam’iyya mai mulki ce ta fara fito da wannan salo da ya ci karo da dokar INEC.
Allah dai muke roko da ya zaba mana shugabanni nagari ba don halinmu ba, don Sayyidina Rasulullah sallallahu alaihi wa sallam.
Shamsi Umar Bakanike Dambatta
Toh wannan abu sai dai muce Allah ya kaimu lokachin mugani na tabbar da cewa babu wannan doka duba da yadda jam’iyya mai mulki ce ta nemi hakan da dai jam’iyyar adawa ce ta nemi hakan sai mu yadda da wannan magana da hukumar zabe ta kasa INEC ta yi mu dai fatammu dai akoda yaushe shi ne Allah [S.W.T] ya zaba mana shugabanni nagari masu tausayin al’umma.
Abban Goba
Duk wasu kulle-kulle da za a yi a kowace jam’iyya indai ba alkhairi ba ne Allah ya kifar, ya yi mana zabi na alkhairi
Nuruddeen Muhammad Funtua
A gaskiya wannan salon da APC ta dauko hakan ya nuna cewa akwai luje cikin nadi domin in da sun shirya yin gaskiya to yakamata su bayyana wa mutane gaskiyar wanda zai zama mataimaki, mu dai fatan mu Allah duk wanda zai zama cikas ga kasarmu Allah karka bashi. Allah ya baiwa wanda yake tausayin mu Allah ya zaba mana mafi alkairi ko daga wanne yanki yake
Sadeek Rufa’i Ɗanguguwa
Nijeriya Jaga-jaga, inji wani tsohon wamaki, bashakka wannan batun ya alamta mana cewar shugabancin wannan kasa sam-sam basu shirya wa mulkin wannan kasa ba ko kadan. Sai fatan Allah ya kawo mana mafita ta alkairi.
Amb Ibrahim Adam Dan-Sarauta
Badi ba rai kenan, a Nijeriya ne kullum da sabon abinda zai bullo, yau za ka ji shugaba wane ya ce abu kaza, gobe kuma za ka ji wani ya fito da na shi daban.
Amma ni a fahimtana tunda har ki ka ga wancen batun na mataimakin shugaban kasa ya zo a wannan salon, to lallai akwai yiyuwar salon zai taka rawa a siyasance. Allah dai ya zaba mana shugabanni na gari.
Justice Mudansir
Atiku abubakar ya burgeni kuma wannan alamu ne na nasararsa, Alhaji Atiku Abubakar a shekarar 2023, dalilina kuwa shi ne, yakamata a samu barakar neman murdiya ta bangaren PDP, amma sai gashi a Jam’iyya maici ta APC ake kokarin aikata aikin da ya sabawa dokar hukumar zabe ta kasa wato INEC idan har kuma shugaban nata ya amince to zamu ce sayansa jam’iyyar APC ta yi
Sani Ladan
Wannan abin mamaki da yawa yake, to amma mudai masu sauraro ne hakika zan so ace naga karshen wannan shirin da jam’iyyata take yi domin zamu iya kiran ta sabuwar dabarar siyasa a kasata, INEC da APC muna jira muga yadda za ta kaya.
Muhd Basheer Sa’ad
Wannan ai alama ce ta cewar wannan jam’iya son ran ta kawai take yi, kuma tana takama ne da cewar gwamnati a hannun ta take. Kuma hakan raina dimokaradiyya ne tunda dai babu hakan a cikin kudin tsarin dokar zaben kasar.
Yusuf Muhammad Jalingo
Mudai mun san babu wannan acikin doka kamar yadda INEC ta fada amma zamu jira mu ji in tusa zai hura wuta
Muhd Basheer Sa’ad
Wannan ai alama ce ta cewar, wannan jam’iyyar son ran ta kawai take, kuma tana takama ne da cewar gwamnati a hannun ta take.
Kuma hakan raina Demokaradiyya ne tunda dai babu hakan a cikin kudin tsarin dokar za6en kasar.
Yusuf Muhammad Jalingo
Mudai mun san babu wannan a cikin doka kamar yadda INEC ta fada amma zamu jira muji in tusa zai hura wutaaisha