Shekaru 10 da suka gabata, Rahama Sadau ta fito a cikin shirinta na farko a masana’antar Kannywood mai suna ‘Gani Ga Wane’, inda ta fito a matsayin jaruma mai tasowa a wancan lokacin. Tun daga wancan lokacin ne jarumar ta fito a fina-finai fiye da 100 da suka hada da wadanda ta fito a masana’antun shirya fina -finai na Nollywood na Nijeriya da kuma Bollywood ta kasar Indiya.
Jarumar wadda ta samu kwalin karatun digirin-digirgir a jami’ar Eastern Mediterranean Unibersity da ke Arewacin Cyprus, tana daga cikin jaruman da suka kware wajen magana da harsunan duniya daban-daban da suka hada da Turanci, Indiyanci, larabci da kuma Hausa cikin natsuwa da kwarewa, Jarumar ta samu nasarori da dama a cikin shekarun da ta kwashe tana harka ta shirin fim, ta zama mace ta farko a tarihi a masana’antar Kannywood da ta samu shiga manyan fina-finan kasar Indiya na Bollywood, daga cikin manyan fina-finan da ta fito akwai Khuda Haafiz, inda ta fito tare da jarumin Bollywood, Bidyut Jammwal da Up North, Sons Of The Caliphate, Postcards da sauran makamantansu.
- Kabilar Bayankole Da Innar Amarya Ke Jima’i Da Ango Domin Gwaji
- Jihar Gombe Za Ta Rungumi Shirin Farfado Da Noman Auduga Na Gwamnatin Tarayya – Inuwa
Sadau ta zama gwarzuwar jarumar Kannywood a shekarar 2014, bayan da ta fito a wani shiri mai suna ‘Sabuwar Sangaya’, bayan nan ta fito a manyan fina-finan Kannywood kamar ‘Mati Da Lado’, Rariya da Rumana.
Ranar 3 ga Oktoba 2016, kungiyar shirya fina-finai ta Nijeriya (MOPPAN), ta dakatar da ita daga shiga duk wata harka ta kannywood, saboda fitowar da ta yi a wani faifan bidiyo na soyayya tare da mawaki, Classik K, amma a watan Janairu 2018 ne aka dage haramcin da aka sa mata sakamakon sa hannun da gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya yi.