Kasar Sin ta samu karuwar bukukuwan baje kolin masana’antu da fasahohi a shekarar 2024, a cewar wani rahoton da aka fitar a yau Juma’a.
Rahoton na tattalin arzikin baje kolin kasar da kwamitin bunkasa harkokin cinikayya ta kasa da kasa ta kasar Sin ta fitar ya ce, a bara, kasar Sin ta gudanar da bukukuwan baje kolin masana’antu da fasahohi 1,064, adadin da ya karu da kashi 63.4 cikin dari bisa na shekarar 2023.
Rahoton ya kuma bayyana cewa, bikin baje koli ya zama wani muhimmin dandali na nune-nunen nasarorin da sabon karfin samar da hajoji da hidimomi na kasar Sin ya samu, inda masana’antu masu tasowa da masana’antu na gaba suka zama shararrun jigajigan bukukuwan baje koli a bara. (Mohammed Yahaya)