RAHOTO: An Yi Kira Ga Al’ummar Musulmi Su Amince Da Rigakafin Foliyo

Daga Abdullahi Usman, Kaduna

Babban Malamin Addinin Musuluncin nan da ke zaune a Kaduna, Sheikh Dakta Ahmed Abubakar Gumi ya yi kira ga al’ummar musulmi akan su yarda da allurar rigakafin cutar shan-inna don lafiyar ’ya’yansu.  Sheikh Dakta Gumi ya yi wannan kira ne a wajen bude baki a gidansa, wanda kungiyar ’yan jarida masu wayar da kan jama’a akan cutar shan-inna (JAP) suka gabatar a makon da ya gabata.

Malamin ya bayyana cutar shan-inna da cewar cuta ce ta duniya da ke bukatar hadin kan kowa don a kawar da ita.

Saboda haka Sheikh Dakta Gumi, wanda har ila yau Likita ne ya yi kira ga iyaye akan su hada hannu da jami’an kiwo lafiya, kuma su tabbata sun bayar da ’ya’yansu don karbar rigakafin domin a sami nasaran kawar da cutar baki daya a Nijeriya.

Ya ce rigakafin da ake yi wa yara ba shi da illa don dai taimaka wa yara ne wajen kara masu koshin lafiya.

Daga nan sai Malamin ya yaba wa gwamnati da kungiyar ‘Debelopment Partners,’ da sauran masu ruwa da tsaki a fannin lafiya don kokarin da suke yi na neman kawar da wannan cuta da sauran cututtukan da suka addabi yara kanana.

Tunda farko a nasa jawabin, Shugaban kuniyar ’yan jarida masu wayar da kan Jama’a dame da muhimmancin alluran rigakafin ta jihar Kaduna (JAP), Alhaji Lawal A. Dogara ya bayyana cewa kadan daga cikin ayyukansu, sun hada da hada tarukan ilimantarwa ga Jama’a, da shirya wasannin kwaikwayo don fadakarwa ga jama’a.

Exit mobile version