Har kullum kasashen yammacin duniya na nacewa manufofin nuna yatsa ga kasar Sin, ta hanyar fakewa da yayata dimokaradiyya, ko kare hakkin bil adama, duk kuwa da irin nasu tarin matsalolin na cikin gida.
A baya bayan nan, wani rahoto da Tarayyar Turai EU ta fitar mai taken “Rahoton shekara game da yankin musamman na Hong Kong na shekarar 2021”, ya kunshi bayanai masu tarin yawa, da EUn ke ikirarin haka ya kamata kasar Sin ta rika tafiyar da harkoki a yankin na HK.
Wannan rahoto, wanda shi ne irinsa na 24 da EUn ta fitar, na kunshe da kalamai na yaudara da suka saba da gaskiya, ciki har da zargin wai “yanayin kare hakkin bil adama na kara tabarbarewa a yankin na HK”.
Amma abun tambaya a nan shi ne, ko Tarayyar Turai EU, ta taba fitar da makamancin wannan rahoto game da HK cikin shekaru sama da 140 da Birtaniya ta mulkin yankin, karkashin mulkin danniya da watsi da dimokaradiyya?
Idan da a ce kasar Sin ce ta fitar da makamancin wannan rahoto, game da bukatar gyara yanayin gudanar da mulki a Turai, da magance matsalolin dake yawan haifar da zanga-zanga, da fito-na-fito da mahukunta a Turai, da gazawar gwamnatocin Turai wajen shawo kan annoba yadda ya kamata, manya kasashe mambobin EU za su yi maraba da wannan rahoto?
Kowa ya sani cewa, a lokuta mabambanta, wasu daga kasashe mambobin kungiyar EU, sun fuskanci matsalolin tsaro makamantan wadanda Sin ta fuskanta a yankin musamman na HK. Ga misali, kasar Faransa ta sha fama da zanga zanga da fito-na-fito sakamakon dalilai na siyasa, tun daga watan Nuwamban shekarar 2018. Ya zuwa tsakiyar shekarar 2019, tashe-tashen hankula sun haifar da rasuwar mutane 11, da jikkatar fararen hula 2,500, baya ga jami’an tsaro 1,800 da su ma suka jikkata. Kaza lika an cafke adadin mutane da yawansu ya kai sama da 8,000.
Rahotanni sun ce an yi amfani da karfin tuwo wajen tabbatar da doka da oda. Inda mahukuntan Faransa suka rika barazanar daukar matakan ba-sani-ba-sabo kan masu tayar da kayar baya.
Sai dai abun mamaki a nan shi ne, da yawa daga kafofin watsa labaran kasar Faransa, sun rika kiran barnata gine-gine da masu zanga zangar suka yi a birnin Paris a wancan lokaci, da aikin tsageru, amma a daya hannun, sun rika kiran matakin lalata zauren majalisar dokokin yankin HK da masu zanga-zanga suka yi da “jarunta” shin wannan ba nuna fuska biyu ba ne?
Amfani da irin wannan mizani 2 wajen kwatanta abubuwa makamantan juna, da wariya, da kaucewa adalci daga gwamnatoci da kafafen watsa labaran kasashen yamma suke yi, ya yi daidai da karin maganar Bahaushe dake cewa “Laifi tudu ne, ka take naka ka hango na wani”.
Har kullum, sassa daban daban na kasashen yammacin duniya na yawan maimaita muhimmancin kare hakkin bil adama. Amma sun mance cewa, lullube laifukan da suke aikatawa na keta hakkin bil adama, da kokarin ganin baiken kasar Sin kan hakkin bil adama, yana kara fallasa aniyar su ta siyasantar da batun hakkin bil adama. Kuma irin wadannan rahotanni masu cike da kage, da rashin adalci da EU ke fitarwa, ba za su sauya hakikanin gaskiyar da dukkanin al’ummun duniya suka sani ba. (Fa’iza Mustapha)