Wani rahoton taron dandalin tattauna harkokin kudi na duniya (IFF), ya ce ana sa ran alkaluman tattalin arzikin kasar Sin wato GDP, zai karu da kaso 5.2 a bana, kana zai karu da kaso 5 a shekarar 2024.
An fitar da rahoton na IFF kan harkokin kudi da ci gaban duniya na shekarar 2023 ne yayin taron shekara-shekara da murnar cikar dandalin shekaru 20 da kafuwa, wanda aka yi jiya Asabar a birnin Guangzhou na lardin Guangdong na kasar Sin.
- Ministan Harkokin Wajen Sin Ya Tattauna Da Masana Tsara Manufofi Da ’Yan Kasuwa Na Amurka
- Xi Jinping Ya Gana Da Gwamnan Jihar California Dake Amurka
Rahoton ya kuma yi hasashen ci gaban tattalin arzikin duniya zai ci gaba da tafiyar hawainiya a bana, a kan kaso 3.1, kuma akwai yuwuwar zai ci gaba da kasancewa a mataki mara kwari a shekarar 2024.
IFF taron dandali ne mai zaman kansa na kasa da kasa da shugabannin cibiyoyin hada-hadar kudi na kasashe da yankuna sama da 20, da suka hada da Sin da Amurka da Tarayyar Turai da kasashe masu tasowa da shugabannin hukumomin kasa da kasa kamar MDD da Bankin Duniya da asusun ba da lamuni na duniya wato IMF, suka kafa a watan Oktoban shekarar 2003, a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin. (Fa’iza Mustapha)