A ranar Litinin ne, hukumar kula da tattalin arzikin Afirka ta Majalisar Dinkin Duniya (UNECA), ta gabatar da Rahoton Tattalin Arziki na Afirka a 2023 (ERA 2023) inda ya bayyana cewa, akwai bukatar yin kwarya-kwaryan gyaran fuska domin samun ci gaba mai dorewa da kuma jajircewa don cimma nasarar da ake fatan gani.
Daga cikin abubuwan da rahoton ya ce ya kamata a mayar da hankali a kai akwai bukatar kasashen yankin su gano hanyoyin da za su yi hadin kai da aiki da sahihan dabaru na habaka harkokin masana’antu.
Rahoton mai taken: “Gina gurbin Afirka da ya dace wajen bunkasa tattalin arzikin duniya”, wanda Darakta mai kula da harkokin tattalin arziki da mulki a hukumar (UNECA), Adam Elhiraika, ya gabatar, ya nuna cewa, tsarin ci gaban tattalin arzikin duniya a halin yanzu yana ba da mamaki ga kasashen Afirka bisa yadda suke da bukatar hanzarta habaka masana’antu ta hanyar yin gwaji da kyau kan abin da zai fi zama mafita gare su da kuma yadda za su daidaita lamarin bisa tsarinsu na gida.
Elhiraika ya bayyana cewa, ci gaban da ake samu a Afirka yana da alaƙa da fitar da kayayyaki, yin aiki da manyan kasashen duniya da kamfanoni, da bin ka’idoji da kuma haɓaka ƙungiyoyin masana’antu.
Waɗannan abubuwa, bisa ga rahoton na ERA 2023, ana bukatarsu a bangarori daban-daban ta fuskar ire-iren kamfanonin da ake da su da kuma ƙarfin fasaharsu.
A nashi bangaren, Babban Jami’in Majalisar Ɗinkin Duniya a Nijeriya, Mista Matthias Schmale, wanda Masanin Tattalin Arziki, Nonso Obikili, ya wakilta, ya lura cewa abubuwa marasa dadi daban-daban, kamar illolin da annobar COVID-19 ta haifar, da yunkurin mamayar da Rasha ke yi a Ukraine, da sauyin yanayi sun sa Afirka ta fuskanci koma-baya wajen cimma muradun ci gaba mai dorewa na duniya (SDGs).
Ya ba da misali da yadda talauci a cikin 2021 ya karu sosai, lokacin da kusan ‘yan Afirka miliyan 30 suka fada kangin matsanancin talauci, inda hakan ya haifar da asarar ayyuka miliyan 22.
“Kasashe goma da suke da mafi yawan matalauta sun kai kashi 64.7% na nahiyar. Kasashe hudu na farko—Nijeriya (miliyan 100), Jamhuriyar Demokuradiyyar Congo (miliyan 67), Tanzaniya (miliyan 36), da Habasha (miliyan 33)—sun dauki kashi 42% na talakawa da kef ama da talauci.” In ji Schmale.
Don haka, ERA 2023 ya yi kira da a samar da sabbin dabaru ga kasashen Afirka don magance kalubalen matsalar tattalin arzikin duniya. Rahoton ya yi kira da a inganta yadda ake magance matsaloli da samar da jajircewa ta hanyar tsare-tsare masu kyau na ci gaban kasa da shugabanci nagari, da kuma kawo sauyi ga tsarin ci gaban masana’antu.
Bugu da kari, mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin tattalin arziki, Dokta Tope Fasua, ya bayyana koma-bayan tattalin arzikin da Nijeriya ta samu tun a shekarun baya da suka hada da: hauhuwar farashin kayayyaki a farkon shekarun 1970 bayan tashin gwauron zabon farashin mai a shekarar 1973; koma bayan shekarun 1980 saboda faduwar farashin kayayyaki; da kuma wani matsalar da aka samu a tsakiyar shekarun 2000 sakamakon faduwar danyen mai.
“Muna rayuwa cikin rashin daidaito ta fuskar tattalin arzikinmu, kuma yawancin Afirka har yanzu suna fama da irin wannan matsalar.” In ji shi.
Daga cikin wadanda suka halarci taron gabatar da rahoton akwai wakilan ofishin jakadancin Amurka, Tarayyar Turai, Sashen Bunkasa Ci Gaba na USAID, Ma’aikatar Kasafi da Tsare-tsaren Tattalin Arziki ta Tarayya, Ma’aikatar Kudi, Babban Bankin Nijeriya da kuma hukumomin Majalisar Dinkin Duniya.
Wannan rahoto dai ya sake nuna yadda ake barin Nahiyar Afirka a baya ta fuskar hada-hadar kasuwanci a duniya duk da cewa akwai tarin albarkatun kasa da Allah ya huwace wa yankin inda ake danganta hakan da rashin samun shugabanci nagari a yankin.