Wata majiya ta tsegunta mana cewa Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa a Nijeriya (NEMA) ta tattara wani rahoto kan zanga-zangar yaƙi da fatara da yunwa da matsin rayuwa da aka gudanar a rana ta farko, ranar Alhamis 01 ga Augustan 2024.
Rahoton na NEMA ya ce:
1. Rasuwa – Mutane 21
2. Raunika – Mutane 175
3. Waɗanda aka kama: Mutane 1,154
3. Jihohin da aka saka dokar hana fita sun haɗa da:
1. Yobe
2. Maiduguri
3. Kano
4. Jihohin da aka samu hatsaniya da faɗace-faɗace sun haɗa da:
1. Abuja
2. Adamawa
3. Bauchi
4. Bayelsa
5. Kuros Ribas
6. Gombe
7. Kaduna
8. Kano
9. Katsina
10. Kebbi
11. Legas
12. Osun
13. Neja
14. Rivers
15. Zamfara
16. Borno
17. Yobe
5. Jihohin da aka gudanar da zanga-zanga cikin lumana sun haɗa da:
1. Filato
2. Taraba
3. Delta
4. Ebonyi
5. Edo
6. Benuwe
7. Nasarawa
8. Abiya
10. Ogun
6. An tafka asarar dukiya da ta kai: Naira Biliyan 6