A daidai lokacin da matasan Nijeriya ke gudanar da zanga-zangar tsadar rayuwa da matsin tattalin arziki a Nijeriya, masana sun nuna cewa, zanga zangar ba zai dawo da tattalinarzikin kasa yaddayake a da a cikin gaggawa, saboda haka ya kamata al’umma su samar wa kansu hanyoyin ci gaba da fuskantar wadannan matsalolin Wakilinmu ya zakulo muku wasu shawarwari da dabaru da masana suka fitar wanda mutane za su iya amfani da su domin rage radadin matsin da ake fuskanta.
1. Idan wuri ba shi da nisa, to a daure a taka a kafa. Yin hakan zai kara lafiyar jiki da kuma kiyaye ‘yan kudade.
2. Akwai kayan abinci masu kosarwa da basu bukatar a dora su a wuta; kamar garin kwaki da sukari, da ‘yar gyada mai gishiri. Idan a inda kake akwai gurasa ita ma za ta kashe yunwa ba tare da an kashe kudade da yawa ba.
3. A rage yin baki da kuma kai ziyara har sai idan ya zama dole. Idan za a kai wa wani ziyara a rika sanar tun kafin lokacin ziyarar. A karfafa zumunci ta wayar salula.
4. Idan za a dafa shinkafa a jika ta sosai, kafin a dora ta a wuta. Sannan yayin da take kan wuta a sa ido sosai.
5. A guji barnar kudi wajen sayen naman miya. Amfani da wake ko ganye kamar alayyaho yafi rahusa da kuma kara lafiyar jiki.
6. A rika dora zogale, ko tafasa a abinci suna hanzarta koshi da kara lafiya.
7. Duk kwan lantarki ko kyandir a tabbatar an kashe su, kada a kunna sai daidai lokacin da ake bukatar haske.
8. Indomie tana da sauki da kuma rahusa. Amma a kiyaye gishirin da ke cikinta, domin yana da illa.
9. A rika amfani da mizani ko sikeli wajen tantance kayan abincin da za a yi amfani ko za a dafa a gida. Hakan zai rage barna da kuma tabbatar abin da aka dafa daidai yake da bukata.
10. Ba dole ba ne a ci abinci sau 3 a kowacce rana, idan har babu yunwa ko sau biyu 2 kawai aka ci abinci babu laifi.
11. Gero, dawa da masara suna bukatar hidima sosai kafin su zama abinci. A guje su dukka, sai dai idan babu wani zabin.
12. Danwake yana da nagarta wajen kashe yunwa, kuma ba ya bukatar hidima sosai.
13. Dumame yana da albarka. Idan abinci ya yi saura a tanade shi domin da safe a yi dumame.
14. Idan akwai beraye a gida a tabbatar an halaka su da guba mai karfi. Baraye suna yin barnar kayan abinci da kuma sacewa.
15. Idan har kana da wayar salula baka bukatar agogo; idan kana da agogo ka sayar a sayo wani abu mai amfani.
16. A dakatar dayin sabuwar sutura, na dan wani lokaci, sai dai idan ya zama dole. A takaita yawan yin sutura. Kufta tana da karko da jimawa.
17. Wajen girki, amfani da gawayi yafi sauki.
18. Idan maigida ya je kasuwa ya tarar farashin kayan abinci ya karu, koda kadan ne, to a sanar da uwargida, domin ita ma ta san halin da ake ciki. Haka zai taimaka wajen tsumin abinda ake da shi da kuma kyautata tattalin arzikin iyali.