Wani al’amari mai ban tsoro da ke faruwa a halin yanzu shi ne, yadda babu zato babu tsammani, ba kuma tare da wata alama ba; kwatam, sai ka ga maza sun fadi ringis; sun kasa mikewa.
A cikin shekarun baya-bayan nan, mun ga yadda wasu maza lafiyayyu; masu kuzari a jiki ke faduwa yayin gudanar da ayyukan motsa jiki. Wannan al’amari mai tayar da hankali, na ci gaba da yawaita a tsakanin al’umma tare da kawo mana bakin ciki a cikin rayuwarmu.
- Kidayar Jama’a Da Harkar Lafiya
- Sin Ta Yi Maraba Da Amincewar Da UNGA Ya Yi Da Kudurin Wanzar Da Zaman Lafiya Da Kasar Ta Gabatar
Haka zalika, ba wai maza kadai ne irin wannan mutuwa ta fuju’an ke faruwa da su ba; har ma da matan, illa kawai dai na mazan ya fi rinjayar na mazan a zahiri.
A ‘yan shekarun nan, wani abin bakin ciki da takaici da har yanzu yana nan a raina shi ne, wani dan’uwan maigidana ne; wanda a zahiri mutum ne lafiyayye kuma dogo, dan wasan kwallon kwando, ya kasance kuma tauraro a kwallon kwandon; wanda yake wakiltar jiharmu da kuma kasa baki-daya.
Har ila yau, duk wanda ya kalle shi; zai ga lafiya ce ke tafiya karara tare da sha’awarsa; sakamakon ganin sa da ake yi yana motsa jiki a kowace yamma ta duniya, amma sai rashin sa’a ta taru da shi a ranar wata Alhamis, inda babu zato; babu tsammani ya yanke jiki ya fadi a filin wasa yana dauke da Azumi, tun daga nan bai sake motsawa ba; haka muka rasa shi.
Haka nan, Dakta Mahmoud Muhammad; tsohon babban likitan asibitin IBB, sannan kuma tsohon babban sakatare a Jihar Neja, wanda shi ma tasa mutuwar ta yi matukar girgiza al’umma, wanda a cikin wani bidiyo mai tayar da hankali ya nuna shi cikin kuzari, yana buga kwallo a wani filin kwallo; kamar wani kwararren dan wasa, amma kafin kiftawar ido; ya fadi kasa, kamar wanda ya gaji yake son hutawa, sai kuma wannan ce kwanciyar tasa ta har abada.
Kazalika, shi ma wani sanannen matashi dan Kannywood; mai cike da kuzari, El-Muaz Muhammad; ya rasa rayuwarsa yayin da yake yin wannan wasa na kwallo, inda nan take ya fadi babu zato; babu tsammani, daga nan kuma sai ya ce ga garinku.
Irin wadannan abubuwan bakin ciki, na ci gaba da yawaita a takanin al’ummarmu. Wannan yasa nake tambayar abin da ke haddasa ire-iren wannan mutuwa ta fuji’an a tsakanin mazajenmu.
A matsayina na Musulma, na yarda da fadin Allah SWT cewa; “Kullu nafsin za’ikatul maut”, ma’ana; kowane mai rai zai dandani mutuwa, kuma babu wanda zai bar duniya kafin lokacinsa ya yi, amma duk da haka kuma, imaninmu ba zai taba cire mana alhakin kula da lafiyarmu ba.
Wadannan asarar rayukan da muke yi na mazajenmu, dole ne na yi kira da mu farka, musamman ma ga maza; wadanda galibi ke yin sakaci wajen kula da lafiyarsu, suna barin matansu na ci gaba da kasancewa a matsayin zawarawa; ‘ya’yansu kuma na zama marayu.
A al’ada, mun yarda da cewa; mutuwa ba ta da makawa, duk wanda lokacinsa ya yi; wajibi ne ya tafi. Sai dai abin mamaki kuma shi ne, yayin da muke kokarin jinkirta ko kauce mata, wasu daga cikin ayyukanmu na rashin sani; kan sanya mu matsa kusa da ita da gangan. Misali, muna kula da motocinmu da kyau kafin mu fara tafiya da su, haka nan ba za mu taba kwanciya a kan hanya ba, saboda zai kasance tamkar kisan kai ne.
Amma duk da haka, maza da yawa na yin sakaci da lafiyarsu, ba tare da suna kula da ita yadda ya kamata ba, suna kai kansu ga hadarin da ya kamata su rika gujewa.
A lokacin da nake aiki a ofishin jin kai na Asibitin Suleja, na lura da bambanci mai ban mamaki. Ofishinmu na kusa da dakin kula da masu ciwon hawan jini, a nan ne na fara lura cewa; galibin marasa lafiya mata ne. Wannan yasa na yi tunanin cewa, mata sun fi maza samun cutar hawan jinni; saboda damuwar da ke tattare da aure da rainon yara ga uwa.
Amma daga bisani, sai na gano cewa; yayin da mata ke zuwa neman magani idan ba su da lafiya ko suna dauke da juna biyu, maza kan yi shiru ne da bakinsu, ciwo na damunsu amma saboda kokarin nuna jarumta; sai su yi shiru har sai ya illata su.
Don haka, ya kamata maza su sani cewa; mu danginku muna bukatar ku cikin koshin lafiya, bai kamata ku rika sadaukar da rayuwarku; kuna matsa wa kanku wajen yin aiki tukuru ba, alhali jikinku yana son hutu.
Ku fara da yin gwaje-gwajen lafiyarku akai-akai a asibiti ko kuma a gida. Yanzu Bature ya kawo mana sauki, domin kuwa za ka iya sayen na’ura mai sarrafa kanta a cikin sauki wajen gwajin hawan jini da ciwon suga, sannan wannan na’ura za ta iya taimaka muku wajen samun bayanai ko shawarar ganin likita nan take; ko kuma batun daukar huta kafin ci gaba da motsa jikin da kuke yi na yau da gobe.
A nan, ba wai ina cewa wannan zai maye gurbin shawarar likita ba ne, amma zai iya zama tamkar wata fadakarwa ce mai matukar amfani; don neman taimakon gaggawa.
A takaice dai, ku kasance kuna cikin koshin lafiya; ku rika samun lokacin hutawa yadda ya kamata, sannan kuma ku tabbata kun kasance masu bayyana wa wadanda kuka yarda da su matsalolin da suke addabar ku.
Akwai alamomin da jikinku zai fada muku a daidai lokacin da kuke bukatar hutu; ku yi na’am da wannan sako, domin rayuwarku kyauta ce; lafiyarku kuma ba kawai taku ba ce, har ma da wadanda ke kaunarku.
Mazaje a manta da jarumtaka a bai wa jiki hakkinsa. Ku tabbata kuna hutawa a duk yayin da kuka gaji, idan jiki na yi muku ciwo; a yi maza a ga likita. Ba ma bukatar jarumtakarka, domin mun fi mukatarku da rai da kuma koshin lafiya.