Kamar yadda masana a baya cikin wannan rubutu aka hakaito suna masu fadin cewa, jan-kafa cikin sabgar kidayar, kan zama silar rashin samun nasarar kyawawan tsare-tsare da ake shiryawa, don inganta fannin lafiya a kasa. Babu shakka, wannan wani abu ne da za a yi saurin fahimta, yayin da aka yi la’akari da wasu abubuwa kamar haka;
Likita Guda Zai Jibinci Duba Marasa Lafiya Dari Shida A Asibitoci
- Dimokuradiyyar Jama’a Da Ta Shafi Matakai Daban Daban Wani Muhimmin Tabbaci Ne Ga Ci Gaban Kasar Sin
- Mai Da JamaA A Gaban Komai, Jigon Tsarin Raya Birnin Fuzhou
A ka’idance, kowane likita guda, zai duba marasa lafiya guda dari shida (b00) ne cifcif, kamar yadda Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta nusar a cikin wannan Shekara ta 2024. Ga tambaya, ba tare da an san adadin yawan jama’ar kasa ba, ta yaya ne za a iya fitar da adadin yawan likitocin da ake da muradi a kasa, tare da ba su adadin marasa lafiyar da za su duba daidai-wa-daida?.
Kuma a fili ne yake cewa, rashin dabbaka waccan ka’ida ta hukumar lafiyar ta Duniya, WHO, na iya haifar da abubuwan-ki birjik a bangaren na lafiya, wanda zai shafi mai dubawar, da wadanda za a duba din. Wani abin takaici a yau cikin wannan kasa, ta tabbata cewa, duk likita guda daya, na yin tiri-tiri ne da marasa lafiyarmu har kimanin mutum dubu tara da tamanin da uku (1:9,083) ne. Shin, a duk sa’adda likita ya gaji, tare da rashin samun cikakken hutu, hakan ba zai kawo wata illa ko wani nakasu yayinda yake duba marasa lafiya ba?.
Adadin Asibitoci Da Kayan Aiki
Tsakanin gari A, da ke kunshe da mutane dubu dari biyar (500,000), da kuma garin B da ke kunshe da mutane kimanin miliyan daya da dubu dari biyar (1,500,000), shin, suna bukatar adadin kayan aiki iri guda ne? Wanne ne zai bukaci adadin kayan lafiya sama da gudan? Zai yu ace adadin gadajen kwanciyar da ke garin A, sune kuma za a kai garin B?. Samsam ba shi yiwo. To idan gwamnatoci ba su da lissafin jama’ar wadannan mabanbantan garuruwa biyu (garin A da garin B), ta yaya ne za ta gudanar da abinda ya kamata?.
Yayin Barkewar Wata Annoba
Lokacin da cutar COBID-19 ta barke cikin Duniya, misali a Nijeriya, ta yaya ne za a raba kayan tallafi bisa dogaro tare da samun daidaito da aiki bisa ilimi, ba tare da sanin adadin yawan mabanbantan mutanen dake zaune a sakuna da lungunan kasar ba?.
Lokacin da aka yi kidayar karshe a wannan kasa ta Shekarar 200b, ta tabbata cewa, jihar Nassarawa na da adadin yawan mutane miliyan daya da dubu dari takwas da sittin da uku, da dari biyu da saba’in da biyar (1,8b3,275). Ita kuwa jihar Plateau, na da adadin yawan mutane miliyan uku (3,000,000) ne. Jihar Lagos kuwa, na da mutane miliyan tara (9,000,000) ne, ita kuwa jihar Kano, na da adadin mutane miliyan tara da dubu dari hudu da “yankai (9,400,000) ne.
Shin, yayin gabatar da kayan agaji na annobar COBID-19 zuwa wadannan mabanbantan jihohi hudu da aka lasafta, za a ba su kayan aiki ne kai-da-kai, ma’ana, za a raba musu kayan tallafin ne daidai da daidai?. Ko kadan hakan ba zai yu ba, dole ne sai an yi la’akari da mabanbantan adadin yawan jama’ar da kowace jiha ke da.
Haka abin yake yayin barkewar annobar amai da gudawa a cikin wadannan jihohi hudu, wajibi ne yayin kai musu kayan dauki daga gwamnatin tarayya, ya zamana an yi la’akari da irin mabanbantan yawan da suke da shi.
Rashin sanin hakikanin adadin yawan mutane a cikin sakuna da lunguna na wannan kasa, dole ne ya rika cutar da abubuwan da suka shafi tsare-tsaren fannin lafiyarmu da ma sauran fannonin rayuwa, kuma, shafa ta cutarwa.
Haihuwa Kyauta A Asibitocin Gwamnati
Shin, adadin kayan aiki na haihuwa da wata gwamnati a jiha za ta samar a mabanbantan asibitoci, saboda kudirin da ta zo da shi na haihuwa kyauta ga mata a asibitocin gwamnati, za su zamto adadinsu na-baidaya ne?. Ma’ana, kayan aiki da za a mika su asibitocin Murtala, da na Sir Muhammadu Sanusi, da na Sabo Bakinzuwo, za su zamto adadi daidai-wa-daida ne?.
Ko ba a fada ba, mai karatu ya kwana da sanin cewa, kayan aikin da za a mika zuwa ga asibitin Murtala, sai ya kere na sauran asibitocin gwamnatin jiha yawa. Haka abin yake, idan gwamnatin Jihar Kano ta tasamma bijirar da irin wadancan kayaiyaki zuwa ga asibitocin kananan hukumomi 44 da ke a jihar ta Kano. Shin, kayan aikin da gwamnatin Jihar Kano za ta samar a kananan asibitocin karamar hukumar Minjibir, gwargwadon yawansu ne ma za a samar a kananan asibitocin karamar hukumar Dala?. Koko adadin kayan aikin da za a samar a karamar hukumar Ghari, gwargwadon adadinsu ne kuma za a samar a karamar hukumar Gwale ko Nassarawa?.
Amsa, a’a. Idan ba haka lissafin yake ba, ta yaya ne za a iya tantancewa tare banbance adadin yawan kayan aikin da za a mika, bisa ilimi ba zato ba, a yanayin da ya kasance gwamnatoci ba sa gudanar da kidayar jama’a da ta gidaje a duk bayan Shekaru goma (10)?. Wanda dole sai an fahimci adadin yawan jama’ar da ke zaune a waje, kana za a iya gabatar musu da wani alherin da zai taba rayuwarsu daidai-wa-daida, ba tare da samun wani ragin-daka ba.
Cikin waccan mukala da aka ambata a baya, wadda kunzumin masana su Faefesa Odiii suka rubuta, sun gabatar da kokwanton cewa, a yanayi na rashin gudanar da aikin kidayar jama’a akai akai a kasa, hakan na nuna rashin tabbas din samun ci gaba mai dorewa a fannin lafiya, tare da rashin cim ma burikan da aka sanya a gaba don inganta fannin lafiya, “Sustainable Debelopment Goals, SDGS”.
Akwai misalai birjik, wadanda za su hakkake rashin riskar ci gaba dorarre a sashen na lafiya, ma-damar an takaita, ko an wayigari ana jan-kafa wajen aiwatar da aikin kidayar jama’a kamar yadda hukumar majalisar dinkin Duniya ta nema da a yi.
Duba da wani kangin rayuwa da kan addabi daidaikun mutane ko kasa baki daya, akan yi amfani da hanyar kaiyade iyali, don samun sawaba da saukin fuskantar wahalhalun karayar tattalin arziki. Ta yaya ne kasa za ta ci moriyar kayyade adadin yawan jama’arta, ba tare da sanin hakikanin adadin yawan wadanda take da su ba?.
Kasashe irin su China da sauransu, ba su kasance suna masu cin moriyar Kayyade iyali ba, face sai ta hanyar sanin hakikanin adadin mutane da Kasar ke da shi a matakin farko. Ko a daidaikun mutane, ka taba ganin wanda ya tasamma kaiyade iyali, ba tare da yana da lissafin sanin adadi ko yanayi da iyalinsa ke ciki ba?.