Mutun uku sun mutu a wani sabon ramin hakar ma’adanai da ya ruguje ya rufto a ranar Alhamis a kauyen Bazakwoi da ke yankin Adnun na Jihar Neja.
An yi nasarar ceto mutum daya da ransa daga ramin ma’adanan da hadarin ya auku.
- Neja: An Ceto Mutane 7 Da Suka Makale Wajen Hakar Ma’adanai
- Ana Bin Masu Hakar Ma’adanai Bashin Naira Biliyan 3.5 A Jihar Kaduna
Darakta Janar na Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar Neja (NSEMA), Alhaji Abdullahi Baba-Arah, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce babu wanda ya maƙale a cikin ramin, inda ya ƙara da cewa an fito da duk waɗanda suka maƙale daga ramin da gudumowar jama’a.
Wannan lamari na ranar Alhamis dai shi ne karo na biyu a irin wannan bala’i a jihar cikin kwanaki 10, wanda idan ba a manta ba mutum 20 sun rasa rayukansu a sakamakon ruftawar ramin haƙar ma’adanan biyo bayan ruwan sama kamar da bakin kwarya a garin Galkago da ke gundumar Shiroro ta jihar Neja a ranar 3 ga watan Yuni, inda wasu 14 suka maƙale a karkashin ƙasa.
Hukumar ‘yansandan jihar Neja ta tabbatar da adadin waɗanda suka mutu, kuma lamarin na baya-bayan nan ya shafi masu hakar ma’adanan da ke gudanar da ayyukan haƙar ba bisa ka’ida ba.